Gwamnoni huɗu da suka isa Kotun Ƙoli

Kotun Ƙolin za ta raba gardama kan takaddamar zaben gwamna a jihohi takwas.

Gwamnoni huɗu da suka isa Kotun Ƙoli

Gwamnoni hudu sun hallara a harabar Kotun Ƙolin domin zaman sauraron hukuncin da za a yanke a wannan Juma’ar.

Gwamnonin sun hada da Bala Mohammed na Jihar Bauchi, Abba Yusuf na Jihar Kano, Caleb Mutfwang na Jihar Filato, da kuma Dauda Lawal na Jihar Zamfara.

Haka kuma, tsohon gwamnan Jihar Filato, Sanata Simon Lalong ya isa harabar Kotun Ƙolin.

Ana dai sa ran kotun za ta yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamna a jihohi takwas da suka haɗa da Legas, Filato, Bauchi, Kano, Abia, Ebonyi, Zamfara, da kuma Kuros Riba.

Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja

Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari

Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi

Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari