Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi
Sarkin ya tunatar da shugabanni cewa shugabanci amanar Allah ce, ba wata dama ta biyan buƙatun kai ba.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa (NTRC), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci gwamnoni, sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da al’umma su ƙara haɗa kai domin magance matsalolin rashin tsaro, talauci da kuma ƙaruwar yara marasa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya.
Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron kwamitin zartarwa na takwas na Majalisar Sarakunan Arewa da aka gudanar a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Ya ce matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin Arewa sun kai matakin da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa tare da haɗin kan kowa.
“Dukkanmu muna cikin damuwa kan abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan. Muna fuskantar matsalar rashin tsaro, talauci da kuma ƙaruwar yara da ba sa zuwa makaranta. Waɗannan matsaloli ne da dole mu haɗa kai wajen magance su,” in ji Sarkin Musulmi.
- An ceto matar marigayi Janar Rabe
- NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana
Ya jaddada cewa sarakunan gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci-gaba, tare da ba gwamnati shawarwari da gudunmawa wajen warware matsalolin da ke fuskantar al’umma.
Sarkin ya bayyana cewa majalisar ta gayyaci Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙara karfafa haɗin gwiwa tsakanin sarakunan gargajiya da shugabannin da aka zaɓa.
“Ba mu yin gogayya da gwamnoni. Mu abokan hulɗa ne. Su ne shugabannin jihohi, mu kuma muna nan ne domin taimaka musu wajen samar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba ga al’ummarmu,” in ji shi.
Sarkin ya tunatar da shugabanni cewa shugabanci amanar Allah ce, ba wata dama ta biyan buƙatun kai ba.
“Shugabanni bayin jama’a ne, ba sarakunan da za su mulki jama’a yadda suke so ba. Ya kamata gwamnoni su ɗauki kansu a matsayin ma’aikatan jama’a, sannan jama’a kada su ji tsoron bayyana musu matsalolinsu,” in ji shi.
Ya kuma buƙaci shugabanni su kasance masu tawali’u da riƙon amana, yana mai cewa dukiyar gwamnati ta jama’a ce.
“Kudin gwamnati ba kuɗin gwamna ba ne. Allah Ne e ke ba wanda Ya so shugabanci, ba don ya fi kowa ba, sai don wata amana ce. Mafi alherinmu shi ne wanda ba shi da girman kai,” in ji Sarkin Musulmi.
Haka kuma ya jaddada muhimmancin addu’a wajen magance matsalolin ƙasa, inda ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da sauran shugabanni addu’a.
“Kada ku daina yi wa shugabanninku addu’a. Da addu’a ta gaskiya, imani da aiki tuƙuru, za a iya kawo ƙarshen rashin tsaro, talauci da rayuwa,” in ji shi.
Sarkin ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa karɓar baƙuncin taron da kuma ƙoƙarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a jihar. Ya ce amincewar Jihar Jigawa da karɓar taron cikin gaggawa ta nuna ƙudurin gwamnatin jihar na ƙarfafa hadin kai da zaman lafiya a Arewa.
Haka kuma ya yi maraba da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da sauran manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron, yana mai cewa halartarsu alama ce ta ƙara karfafa tattaunawa kan harkokin tsaro da ci gaba.
Taron ya haɗa sarakuna, hakimai, manyan jami’an gwamnati, shugabannin hukumomin tsaro da gwamnonin Arewa domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi yankin da kuma samar da hanyoyin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci-gaba.