Gwamnoni ne matsalar Najeriya – Musalla

Wani dan takarar kujerar majalisar dokoki a Jihar Filato, a mazabar Jos ta Arewa Maso Arewa karkashin UPP, Malam Majiburrahman S. Musalla ya bayyana cewa gwamnoni ne matsalar Najeriya a halin yanzu. Musalla, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya. Ya ce gaskiya gwamnonin Najeriya suna nuna son rai tare da […]

Gwamnoni ne matsalar Najeriya – Musalla
Gwamnoni ne matsalar Najeriya – Musalla

Wani dan takarar kujerar majalisar dokoki a Jihar Filato, a mazabar Jos ta Arewa Maso Arewa karkashin UPP, Malam Majiburrahman S. Musalla ya bayyana cewa gwamnoni ne matsalar Najeriya a halin yanzu.

Musalla, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya. Ya ce gaskiya gwamnonin Najeriya suna nuna son rai tare da yin karfa-karfa a harkokin siyasa da harkokin mulki tare da taka kowa a jihohinsu. Kuma sai wanda suke so yake samun mukamin siyasa ko mukaman wasu harkoki na cigaban jama’a.

“Sakamakon wannan karfa-karfa da gwamnoni suke yi ‘yan majalisun jihohi sun zama ‘yan amshin shatansu, sai abin da gwamnonin suke so  suke aiwatarwa. Kuma gwamnonin basa yin wasu ayyuka na cigaba a jihohin nasu”.

Matashin ya ce ya kamata matasa da sauran al’ummar kasar nan, su tashi tsaye don ganin an magance wannan matsala ta gwamnoni a Najeriya.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa