…Gwamnoni sun bijire wa gwamnoni

Tsawon shekaru hudu da suka wuce, kudin kayan abinci da na man fetur ya karu matuka, shin idan muna da tunani ya kamata mu bijiro da bukatar rage kudin ma’aikata?dan majalisar ya ce rage albashin ma’aikatan zai kara yawan cin hanci a tsakanin ma’aikata, ta yadda ma’aikata za su tsunduma wajen aikata miyagun ayyuka don […]

…Gwamnoni sun bijire wa gwamnoni

Tsawon shekaru hudu da suka wuce, kudin kayan abinci da na man fetur ya karu matuka, shin idan muna da tunani ya kamata mu bijiro da bukatar rage kudin ma’aikata?
dan majalisar ya ce rage albashin ma’aikatan zai kara yawan cin hanci a tsakanin ma’aikata, ta yadda ma’aikata za su tsunduma wajen aikata miyagun ayyuka don neman karin kudin shiga.
Ya ce ba tsabagen rashin hankali ba ne ga gwamnonin da ke kashe Naira dubu 18 a abinci guda kawai, sannan su bukaci ma’aikaci da ya karbi albashin kasa da Naira dubu 18 a wata?
Ya ce: “Idan gwamnati ta ki biyan ma’aikata albashi mafi karanci na Naira dubu 18, to sun nuna wa ma’aikata hanyar sata. Idan kuwa har muna son kawo karshen cin hanci da rashawa, dole ne mu biya ma’aikata yadda ya dace.
“Bai kamata ka iya kashe fiye da Naira dubu 18 a kan abinci guda ba, amma ka ce mutumin da ke daukar albashin Naira dubu 18 a wata wai ana biyansa fiye da kima.

Ba mu amince da matsayin gwamnoni ba
– Gwamnatin  Filato

Mista Samuel Emmanuel Nanle shi ne Daraktan Watsa labaran gwamnan Jihar Filato. A wannan tattataunwar da ya yi da wakilinmu, ya yi bayanin matsayin gwamnatin Filato kan matsayar da gwamnonin jihohin kasar nan suka fitar na cewa ba za su iya cigaba da biyan karancin albashi na Naira dubu 18 ba, inda ya ce gwamnatin jihar Filato za ta cigaba da biyan wannan karancin albashi na Naira dubu 18. Ga dai yadda tattataunawar ta kasance:
Daga Hussaini Isah, Jos

Aminiya: Me za ka ce dangane da matsayar da gwamnonin kasar nan suka dauka kan cewa ba za su iya cigaba da biyan karancin albashi na Naira dubu 18 ba?
Emmanuel Nanle:  Gwamnonin jihohin Nijeriya ba su ce ba za su iya cigaba da biyan karancin albashi na Naira dubu 18 ba. Abin da suka ce shi ne, a lokacin da gwamnonin jihohin kasar nan suka amince za su biya ma’aikata karancin albashi na Naira dubu 18, ana sayar da gangar mai a kasuwar duniya kan farashin dala 126, don haka suka ce ganin halin da ake ciki a yanzu na karyewar farashin mai a kasuwar duniya, inda ake sayar da gangar mai kan farashin dala 41, wanda ya kawo matsalolin rashin shigowar  kudade ga gwamnonin, saboda haka suka ce idan nauyin ya yi masu yawa za su duba wannan al’amari na biyan karancin albashi na Naira dubu 18.
Aminiya: To ina matsayar gwamnatin jihar Filato dangane da wannan al’amari?
Emmanuel Nanle: Gaskiyar magana gwamnatin jihar Filato tana iyakar kokarinta wajen biyan wannan karancin albashi na Naira dubu 18. Kuma Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya ce  zai cigaba da biyan wannan karancin albashi. Abin da a kullum yake gaya wa kungiyar kwadago ta jihar nan shi ne, yana kokari ya ga yadda za a bayar da tallafi domin a samu a cigaba da biyan wannan karancin albashi na Naira dubu 18.  Kuma ya ce shi ba zai rage ma’aikata a jihar nan ba.
Aminiya: Wannan ya nuna  Gwamna Lalong ya bijera wa wannan matsaya da gwamnoni suka dauka ke nan?
Emmanuel Nanle: Ai ka san ma’aikata sune karfin jihar Filato. Babu wani abu da ake yi a Jihar Filato wanda ya wuce aikin gwamnati, don haka babu wani wuri da mutane suke samun mafaka kamar aikin gwamnati a nan jihar. Kuma idan ka lura kowane ma’aikaci mutum daya a jihar  nan, za ka samu akalla akwai mutum 8 da suke karkashinsa. Don haka idan ka duba wannan, sai ka ga rabin mutanen Jihar Filato sun dogara da aikin gwamnati ne. Idan ka ce ba za a cigaba da biyan wannan albashi ba, biyan kudin makaranta da abinci da sutura da sauran bukatun yau da kullum  zai yi wa jama’a wuya a jihar nan. Shi ya sa gwamna Lalong ya ce ganin yanayin jihar Filato ya bambanta da kamar jihar Kano wadda take da harkokin kasuwanci wanda yake samar da hanyoyin samun kudaden shiga. Wannan shi ne yasa  gwamna  ya kauce wa wannan magana da gwamnoni suka yi.
Aminiya: To wadanne hanyoyi ne gwamnatin Filato za ta bi wajen samun kudade da za ta cigaba da biyan wannan karancin albashi na Naira dubu 18?
Emmanuel Nanle: Gwamnatin Filato za ta cigaba da kokarin bunkasa harkokin kasuwanci. Don haka a lokacin da Gwamna Lalong ya karbi mulkin jihar nan, ya ce bayan  ya ga an samu zaman lafiya, babban abin da zai sanya a gaba shi ne ya ga  an sake gina babbar kasuwar da ta kone, tare bude hanyoyin zuba jari wadanda mutane za su samu su zuba jari.  Ka ga idan an yi haka za a samu hanyoyin samu kudaden haraji a jihar nan. Idan aka samu kudaden haraji wannan zai tallafa wajen cigaba da biyan albashin.
Bayan haka, muna sa ran idan Allah Ya yarda abubuwa za su gyaru, kuma kudin mai zai kara yin sama.
Aminiya: Wato gwamnatin Filato tana ganin jihohi za su iya biyan wannan karancin albashi na Naira dubu 18 ke nan?
Emmanuel Nanle: Abin da ya sa ake ganin jihohi suna daukar abin da yafi karfinsu shi ne, gabaki daya, musamman gwamnonin da suka gabata,  kowa yana bayar da kwangiloli barkatai, wadanda babu kudaden da za a biya.Wannan ita ce matsalar da ake fuskanta, domin ko mu a nan jihar Filato mun gaji irin wadannan kwangiloli, wadanda idan ka duba za ka ga wadansu kwangiloli ne da ba su da mahimmanci, kuma babu kudaden da za a biya wadannan kwangiloli. Don haka a yanzu idan har gwamnoni za su shirya abubuwansu bisa tsari kan abubuwa masu mahimmanci. A kasafin kudin da za su yi, za su iya ware kudaden albashin ma’aikata da kudaden da za su yi kwangiloli masu mahimmanci. Idan jihohi suka bi wadannan matakai za su iya biyan karancin albashi na Naira dubu 18.
Aminiya: Wace shawara ce gwamnatin Filato za ta bai wa gwamnonin jihohin kasar nan dangane da wannan al’amari?
Emmanuel Nanle: To, shawaramu ita ce, ya kamata a fahimci cewa  wannan gwamnati ta jam’iyyar  APC,  gwamnati ce ta jama’a, wadda dole ne a tashi  a mutunta jama’a a taimake su. Kuma ya kamata a fahimci cewa biyan albashin ma’aikata shi ne ya fi mahimmanci, saboda haka  a yi kokari a shawo kan wannan matsala, sannan  a ci gaba da  sauran abubuwa.