Gwamnonin APC sun yi taro a Jihar Kebbi
An bayyana cewa aƙalla gwamnoni 20 daga cikin gwamnoni 24 na jam’iyyar ne suka gudananar da taron ƙarƙashin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinm
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnonin Jam’iyyar APC sun gudanar da wani taron sirri a gidan gwamnatin Jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi.
An bayyana cewa aƙalla gwamnoni 20 daga cikin gwamnoni 24 na jam’iyyar ne suka gudananar da taron ƙarƙashin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, wanda shi ne gwamnan Jihar Imo.
- Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata
- Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo
An bayyana maƙasudin taron gwamnonin kan cewa za su tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa da wasu batutuwa na jam’iyya mai mulkin ƙasar.
Majiyar tashar Channel TV ta ruwaito cewa, shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda yana Jihar Kebbi amma bai halarci taron gwamnonin ba. A wata sanarwa da aka fitar Nentawe Yilwatda ya ziyarci jihar ne tun a ranar Alhamis.