Gwamnonin Arewa 5, Shugaba Jonathan da Jamiyyar PDP ……

Watan Yulin da ya gabata ya zama watan da ya fi kowane wata a `yan shekarun nan  yamutsa hazo a cikin siyasar jam`iyyar PDP, mai mulkin gwamnatin tsakiya (gwamnatin tarayya) tun bayan ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, lokacin da aka yi bikin zagayowar ranar mulkin dimokuradiyya, ranar da mulkin dimokuradiyyar kasar nan […]

Gwamnonin Arewa 5, Shugaba Jonathan da Jamiyyar PDP ……
Gwamnonin Arewa 5, Shugaba Jonathan da Jamiyyar PDP ……

Watan Yulin da ya gabata ya zama watan da ya fi kowane wata a `yan shekarun nan  yamutsa hazo a cikin siyasar jam`iyyar PDP, mai mulkin gwamnatin tsakiya (gwamnatin tarayya) tun bayan ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, lokacin da aka yi bikin zagayowar ranar mulkin dimokuradiyya, ranar da mulkin dimokuradiyyar kasar nan ya cika shekaru 14, ana yinsa ba kakkautawa, tun bayan da sojoji suka mika mulki a hannun fara hula a ranar 29 ga watan Mayun 1999.
Bikin ranar ta bana tazo a zaman rabin zango a cikin mulkin shekaru hudu  ga kusan akasarin zababbun kasar nan, wadanda suka hada da shugaban kasa da gwamnonin jihohi da `yan Majalisun Dokoki na kasa da na jihohi. Ma`ana akwai gwamnoni masu zangon farko, akwai kuma masu zangon karshe a cikin mulkin shekaru hurhudu sau biyu da tsarin mulkin kasar nan ya tanada.
Ga irin wadancan gwamnoni masu zangon karshe akan karagar mulki nan aka fi jin wancan ya motsa hazo a cikin siyasar jam`iyyar PDP, don ko ba kome suna ganin nan da shekaru biyu masu zuwa, lalle su nemi wani mukami, amma dai ba na gwamnan jiha ba, don shi kam sun yi, sun gama. Ga gwamnoni masu zango farko, ba a ma jin duriyarsu a cikin hada-hadar siyasar kasar nan, don kuwa su babban abin da ke gabansu bai wuce kwantar da kai ba tsakaninsu da gwamnatin tarayya da jam`iyyarsu da kuma mutanensu, ta yadda za su samu tsallake  siradin yadda za su sake samun wata takarar ta gaba.
Wannan dan bayani ya kawo mu cikin irin dambarwar siyasar da ake ciki a jam`iyyar PDP tsakanin gwamnonin Arewa biyar Alhaji Sule Lamido na jihar Jigawa da Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko na jihar Sakkwato da Dokta Ma`azu Babangida Aliyu na Jihar Neja da Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso na jihar Kano da AlhajiMurtala Nyako na jihar Adamawa da shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da jam`iyyar su ta PDP.  Gwamnonin da dukkansu za su yi ban kwana da mulki a shekarar 2015, in Allah Ya kaimu.
Tun bayan samun nasararsu a zaben shekarar 2011, Gwamnonin jihohin Jigawa da Sakkwato da Adamawa, suka kulla wani kawance tsakaninsu, kawancen da ya rika ba su dama suna yin tarurruka a jihohin juna, tarurrukan da sukan fitar da sanarwa bayan taro akan batutuwan da suka shafi harkokin yau da kullum na kasar nan, tun a bara ba wanda zai iya cewa da kai ga inda wadancan gwamnonin uku suka nufa bare abin da suke son su cimmawa. Shi kuwa dama gwamnan Jihar Kano tun kafin zaben 2011, din yake kan darikarsa ta Kwankwasiyya, wadda kowa ya sa ni cewa da ita ya yi yakin neman zabe, kuma da ita ya kai ga nasara.
Gwamnan Jihar Neja ka iya cewa ya shigo tafiyar gwamnoni biyar din ne saboda kasancewarsa shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, da kuma irin yadda shi ya fara cewa akwai yarjejeniyar da aka yi da Shugaba Jonathan a zaben shekarar 2011, cewa ba zai sake neman takara a shekarar 2015, ba, yarjejeniyar da ofishin shugaban kasa ya musanta an taba yinta.
Wadannan gwamnoni yanzu sun daura damara, kuma sun fito karara suna yaki da aniyar Shugaba Jonathan ta Tazarce. Bayan yaki don tabbatar da zaben da kungiya gwamnonin kasar nan suka yi wa Gwamnan Jihar Ribas Mista Rotimi Ameachi a karo na biyu, sabanin zaben da wasu gwamnoni masu goyon bayan Shugaba Jonathan suka ce sun yi wa  Gwamnan Jihar Filato Mista Dabid Jonah Jang, al’amarin da ya raba kungiyar gida biyu, ya kuma jefa ta cikin rudani. A gefe daya kuma wadancan gwamnoni biyar suna zargin irin yadda Shugaba Jonathan ya kankane harkokin jam`iyyar, ta yadda kome sai yadda yake so za a yi, shi kanshi in ji su wata barazana ce a cikin harkokin mulkin dimokuradiyya.
Bisa ga aniyar neman a didaita sahun shugaba Jonathan da shi kanshi mulkin dimokuradiyyar ya sanya yanzu wadancan gwamnonin Arewa biyar suka shiga ziyartar wasu masu fada a ji na kasar nan, irin wannan ziyarar farko da gwamnonin suka fara sun kai ta ne ga tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a gidan gonarsa da ke Otta a Jihar Ogun a karshen wancan makon (ziyarar da tazo `yan awowi bayan shugaba Jonathan ya kai irin ta ga Obasanjon). A ranar Litinin din makon jiya 22-07-13, wadancan dai gwamnoni suka yi irin waccan ziyara ga tsofaffin shugabannin kasar nan da ke Minna, wato Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdussalami Abubakar, kodayake a karshen makon jiyan sun gana da shugaba Jonatahan a fadar shugaban kasa, amma kafin waccan ganawa da shugaban kasa suna da aniyar sukai irin waccan ziyara ga shugabanni da dattawa irin su tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari da mataimakinsa Dokta Aled Ekweme da Janar Theophilus Yakubu danjuma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dukkan wadancan manyan mutane da gwamnonin biyar suka gana da su ko suke shirin ganawa da su, sukan nemesu da lallai su tsawata wa Shugaba Jonathan akan irin yadda a kullum yake yi wa mulkin dimokuradiyya karan tsaye, inda sukan yi nuni da irin halin da ya jefa Jihar Ribas da gwamnanta da mutanenta, akan kawai batun zaben kungiyar gwamnonin kasar nan da aniyar da Gwamna Rotimi ya nuna ta yana son marawa  Alhaji Sule Lamido a cikin takarar neman shugabancin kasar nan a shekarar 2015. Wani batu kuma da sukan tabo, shi ne irin yadda Shugaba Jonathan ya kankane kome a cikin gudanar da jam`iyyarsu ta PDP, ta yadda sai abinda yake so za a yi.
Kodayake shugaba Jonathan da makarrabansa a lokuta daban-daban sun sha nisanta kansu da rigimar da ake fama da ita a jihar Ribas da kuma ta jam`iyyrsu, amma dai a cikin makon da ya gabata an ruwaito yana cewa duk wadannan rigingimu da ake fama da su suna da alaka da zabubbukan shekarar 2015, amma kuma bai fadi wata magana takamaimiya ba akan me gwamnatinsa take ko za ta yi wajen ganin ta kawo karshen tada hazon.
Amma dai kamar yadda na fadi a wannan filin a `yan watannin da suka gabata, duk mai neman shugabancin kasar nan ya koma ga Allah, bisa la`akari da irin yadda Allah Ya rinka bayar da mulkin ga wadanda mutanen kasa basa tsammani. Allah Ya bamu ikon zaben shugabannin da za su fitar da mu daga akubar da kasa take ciki.