Gwamnonin Arewa da batun bunkasa noma da kiwo
A ranar Larabar makon da ta gabata ne a Kaduna, wajen taron kaddamar da sababbin Shugabannin Kwamitin Amintattu da na Zartaswa na kungiyar Tuntuba ta mutanen Arewa, wato ACF, Kwamitocin da suke karkashin shugabancin tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon da tsohon Sifito Janar na `Yan sandan kasar nan Alhaji Ibrahim Ahmadu Commasie, Gwamnan Jihar […]
A ranar Larabar makon da ta gabata ne a Kaduna, wajen taron kaddamar da sababbin Shugabannin Kwamitin Amintattu da na Zartaswa na kungiyar Tuntuba ta mutanen Arewa, wato ACF, Kwamitocin da suke karkashin shugabancin tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon da tsohon Sifito Janar na `Yan sandan kasar nan Alhaji Ibrahim Ahmadu Commasie, Gwamnan Jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmad ya gabatar da wata kasida mai taken “Tattalin arzikin Arewa da ya kubuta daga arzikin man fetur.” A cikin kasidar gwamnan na Kwara, ya fadi cewa muddin aka mayar da hankali akan ayyukan noma da kiwo, to, kuwa ba makawa tattalin arzikin kasar nan zai yi matukar bunkasa, ta yadda samar da abinci zai inganta ba tare da dogaro da arzikin man fetur ba.
Gwamnan, ya tabbatar da cewa samun arzikin man fetur da kasar nan ta yi, ta wata fuska ya taimaka matuka gaya wajen samar da wasu muhimman abubuwan more jin dadin rayuwa cikin hamzari, amma kuma ya ce ta wani gefen ya taimaka matuka wajen yadda aka yi watsi da ayyukan noma da kiwo, fannin da ya ce a da suke kan gaba cikin batun tattalin arzikin tsohon lardin Arewa da ma kasa baki daya, al`amarin da ya sanya a cikin shekaru 20, da fara samun arzikin man fetur aka fara watsi da ayyukan noma da kiwo, alhali duk kuwa da irin muhimmancin da suke da shi a cikin ci gaban kowace kasa yau a duniya.
Hakan in ji gwamnan na jihar Kwara, ba karamar illa take yi wa kasar nan ba, don a fadarsa tun a wancan lokacin kasar nan take kasa ci da kanta ta fuskar abinci, ta kuma dukufa da shigo da abinci, alhali muna da kasar noma mai yalwa da yabanya da yawan al`umma da za a iya noma kowane irin amfani rani da damina, amma an kasa, abin da ya sa aka dogara kacokan wajen shigo da shinkafa da alkama da sukari da kifi da kaji da nama da tumatar.
Ya ci gaba da cewa kididdigar gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa kasar nan na kashe akalla Naira tirliyan daya da biliyan 300 (N1.3tiriyan) duk shekara wajen shigo da abinci da dangoginsa duk shekara, adadin kudin da ya ce sun nunka yawan kudin da gwamnatocin kasar nan uku (gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi dana kananan hukumomi), suka raba awatan Janairun da ya gabata. Daga karshe Alhaji Abdulfatah ya ce, idan da kasar nan za ta dukufa wajen fannin noma don kasuwanci, to, kuwa da tattalin arzikin kasar nan ya bunkasa, kuma da mun daina shigo da abinci, bare kuma dogaro da kudin man fetur.
Mai karatu wadannan kalamai na daga cikin kalaman da gwamnan jihar ta Kwara, jihar da ke cikin jihohin Arewacin kasar nan da suke ’yan gaba-gaba akan kasar noma mai dausayi a tsakankanin jihohin kasar nan a waccan taro na Kaduna. Taron da za ka iya cewa kusan duk Arewa ta hadu, kuma daya daga cikin manufofinsa shi ne samar wa tsohon lardin mafita akan batutuwan da suka jibanci tattalin arzikin kasa da na siyasa da zamantakewa da tsaro da ilmi da sauran matsalolin da suke neman zame wa Arewar tamfar ciwon ajali, inda ake ta ganin gwamma jiya da yau.
A duk lokacin da na ji gwamnoninmu na arewa suna fadin irin albarkatun noma da kiwo da suke damfare a Arewa da kuma irin yadda sukan yi begen ganin yadda za a amfana da su, ni kan yi mamaki da jin irin hakan, ba don kome ba, sai don irin yadda nike ganin wanda zai shige gaba ya ceci rayuwar jama`arsa kuma yana da makaman a hannunsa (bisa matsayinsa na mai cikakken iko) kuma ya rika irin wancan bege na Gwamna Abdulfatah.
Abin da ya sa na ce haka shi ne tun a zamanin zangon farko na mulkin Shugaba Obasanjo (1999 zuwa 2003), da aka fara batun rabon arzikin man fetur gwamnonin jihohin Arewa baki daya suka kafa Kwamitin da ya kunshi kwararru akan ayyukan gona `yan asalin jihohin Arewa irinsu Cif Audu Ogbeh da Dokta Shettima Mustapha da Gwamnan jihar Adamawa mai ci yanzu, da aniyar su bi masu kadin irin hanyoyi da matakan da suka kamata su dauka don farfado da ayyukan noma da kiwo a arewa, wadanda kafin bayyanar man fetur da kudadensu aka kafa harsashin ci gaban da kasar nan take alfahari da su.
Wancan Kwamiti tuni ya mika rahotansa ga jerin wadancan gwamnonin arewa, wadanda tun a shekarar 2007, suka kammala wa`adinsu, in banda gwamnan jihar Kano Injiniya Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso da bai samu dawowa kan karagar mulki karo na biyu a wancan lokacin, sai a shekarar 2011. Daga dukkan alamu, da gwamnonin Arewan da suke jerin farko na wannan mulkin na farar hula, sun dukufa sun fara aiwatar da shawarwarin da wancan Kwamiti nasu Dokta Mustapha suka ba su, to kuwa a yau da ba ka ji gwamnan na Kwara ba yana bayani dalla-dalla akan irin hanyoyin da Arewa za ta bi ta kubuta daga dogaro da kudin man fetur ba.
Idan mai karatu ya ce ai wancan rahoto na su Dokta Mustapha ya zama tsohon labari ga jerin gwamnonin Arewa masu mulki yanzu. To, ai tsakanin 5 zuwa 6, ga watan Diisamban shekarar 2012, Cibiyar Bincike akan Ayyukan Ci gaban Arewa wato ARDP dake karkashin Gidan Arewa dake Kaduna na Jami`ar Ahmadu Bello dake Zariya ta gudanar da wani taro mai taken “Arewa da matakan ci gaba masu dorewa,” inda ta gayyato masana daga fannonin ilmi daban-daban daga kuma sassa daban-daban na Arewa da suka gabatar da kasidoji akan fannin Ayyukan noma da kiwo da Ilmi da Kiwon Lafiya da Makamashi da Ma`adanai da Koyar da Sana`o`in hannu da inganta Kimiya da fasaha, inda bayan fitar da sanarwar bayan taron, aka kuma bi dukkan gwamnonin Arewa 19, aka mika masu cikakken kundin taron da fatan ganin suna fara aiwatar da shi.
Ka ga ashe mai karatu, ba wai matsalolin da suke gallabar al`ummomin jihohin Arewa da yadda za a magance su, shugabannin Arewan suka rasa ba, a`a ruhun yadda za su tallafa wa mutanen nasu ne da suke kurar baya a kusan dukkan kome na ci gaba a tsakankanin al`ummar kasa. Yanzu kuma shi ne lokaci ba sai gobe ba, musamman wajen su mayar da hankali akan ganin bunkasar noma da kiwo, fannin da duk duniya aka yi ittifaki da cewa yana kakkabe fatara a gidan kowa da kasa baki daya. Kamar yadda Hausawa ke masa kira da Noma yanke talauci