Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro
Taron zai mayar da hankali ne kan matsalolin da yankin ke fuskanta.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya isa Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, domin halartar taron gwamnonin Arewa maso Gabas karo na 12 da za a gudanar gobe Asabar.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ne, zai jagoranci taron.
Taron zai mayar da hankali ne kan batutuwan tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma hanyoyin magance matsalolin ayyukan jin-ƙai a yankin.
- Mutum 12 sun nutse bayan sake kifewar jirgin ruwa a Sakkwato
- An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita
Za a yi taron ne na tsawon kwanaki biyu, inda ake sa ran gwamnonin za su bayar da muhimman shawarwari da kuma cimma matsaya kan matsalolin .
A cewar Isma’ila Uba Misilli, Daraktan Yaɗa Labarai na fadar gwamnatin Gombe, bayan taron ne za a sanar da al’umma matakan da aka cimma domin haɗa kai wajen inganta ci gaban yankin.