Gwamnonin arewa su rungumi sulhu da ‘yan bindiga domin samun mafita – Dattawa
Wata Kungiyar Dattawa a Arewa (NEPG) ta yi kira ga gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma da su hada kai da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da sauran jami’an tsaro wajen tattaunawa da ‘yan bindiga a matsayin hanyar kawo karshen tashe tashen hankula a yankin.
’Yan daban daji

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban kungiyar a shiyyar Arewa maso Yamma, Yusuf Abubakar, ya ce kungiyar ta samu kwarin gwiwa ne sakamakon kokarin da ofishin NSA, Malam Nuhu Ribadu da sauran masu ruwa da tsaki suna yi a halin yanzu wajen lalubo matakan da suka dace don dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
“Mun yi farin ciki da matakan da ake ɗauka a baya-bayan nan, na yi tafiya daga Sakkwato zuwa Gusau da kuma daga Funtua zuwa Zariya, na lura cewa hanyar an samu salama.” inji shi.
Ya bukaci gwamnonin da su rungumi tattaunawa a matsayin mafita mafi kyau domin kawo karshen matsalar tsaro da ta mamaye yankin.
Abubakar ya soki wasu gwamnonin da ke ikirarin cewa suna da bayanan sirri kan ‘yan ta’adda amma suka kasa bayar da irin wadannan bayanai ga hukumomin tsaro.
Kungiyar ta kuma yabawa shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin leken asiri, Sanata Shehu Buba, da kuma wasu ‘yan Najeriya da suka dukufa wajen ganin an dawo da zaman lafiya a yankin.
Don haka kungiyar ta bukaci gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da su yi aiki tare da NSA, Ministan Tsaro, da Hafsoshin Soja don ganin an cimma nasarar zaman lafiya.