Gwamnonin Arewa sun gargadi sojoji

Ranar Asabar da ta gabata ce gwamnonin Arewa suka shawarci sojoji da kada su sake kirkiro wata kungiyar Boko Haram sakamakon rikicinsu da ’yan Shi’a a Zariya. Gwamnonin sun bayyana haka ne bisa la’akari da cewa har yanzu ba a kawo karshen Boko Haram ba, ga shi kuma sojojin da ’yan Shi’a na neman sake […]

Gwamnonin Arewa sun gargadi sojoji
Gwamnonin Arewa sun gargadi sojoji

Ranar Asabar da ta gabata ce gwamnonin Arewa suka shawarci sojoji da kada su sake kirkiro wata kungiyar Boko Haram sakamakon rikicinsu da ’yan Shi’a a Zariya.

Gwamnonin sun bayyana haka ne bisa la’akari da cewa har yanzu ba a kawo karshen Boko Haram ba, ga shi kuma sojojin da ’yan Shi’a na neman sake tada wata fitina a Arewacin kasar nan. Idan ba a manta ba, a Asabar din makon jiya sojoji da ’yan Shi’a sun fafata, inda aka hallaka ’yan Shi’a masu yawa tare da kama shugabansu Malam Ibrahim Zakzaky.
Rikicin wanda ya faro lokacin da mabiya Shi’a suka tare hanyar PZ da ke  Zariya a daidai lokacin da Babban Hafsan Sojoji na kasa, Janar Tukur  Buratai ya je zai wuce, ya tada hankalin mutane da yawa. Gwamnar Jihar Borno,  kuma  Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, Kashim Shatima ne ya shawarci sojojin a jawabinsa na bude taron gaggawan da suka yi a  Kaduna.
Ya ce sun damu matuka kan abin da ya faru a Zariya, wanda hakan ya sa suka ga ya wajaba su yi taron gaggawar domin nemo mafita.
“Mun zo Kaduna ne domin mu tattauna wannan abu da ya faru a Zariya, kasancewar mabiya Shi’a na da mutane a kusan duk jihohin Arewa. Dole ne mu tashi tsaye mu ga an samu mafita tun kafin a sake kirkiro wata kungiya irin ta Boko Haram a kasar nan. Yanzu haka muna fama da matsalar Boko Haram, duk da cewa ba muna hada Boko Haram da Shi’a ba ne, amma ba mu son a sake kwatanta kuskuren da aka yi har aka kirkiro Boko Haram. Lokacin da Boko Haram ta fara kai hare-hare a watan Yulin 2009 ga ’yan sanda a Bauchi a ranar 25 da 26 a Maiduguri, mafi yawan ’yan Najeriya suna kallon rikicin matsala ce ta jihohin  Bauchi da Borno. Amma da suka ci gaba da kai hare-hare a jihohin Borno da Yobe sai ya zama matsalar Borno da Yobe kuma kwatsam sai suka kai harin kunar bakin wake a Abuja a shekarar 2012. Tun daga wannan lokaci sai lamarin ya lalace.