Gwamnonin da suka rasu a kan mulki a Najeriya
Gwamonin Najeriya da suka rasu suna kan mulki, tun daga shekarar 199 zuwa yanzu
Rasuwar Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a safiyar Laraba, ta dawo wa ’yan Najeriya da juyayin sauran gwamnoni da suka gamu da ajalinsu a lokacin da suke kan karaga mulki.
Wannan ne ya sanya Aminiya ta tattaro muku su da kuma yadda suka bar duniya a yayin da suke kan mulki.
Kafin Akeredolu akwai wasu gwamnoni uku da suka riga mu gidan gaskiya a lokacin da suke kan karagar mulki.
1- Shehu Kangiwa:
Gwammnan Jihar Sakkwato Shehu Kangiwa shi ne ya fara rasuwa yan akan mulki.
Gwamna Shehu Kangiwa ya rasu ne bayan da ya fado daga kan doki a lokacin da yake buga wasan Polo a watan Nuwamban 1981.
Daga bisani aka rantsar da mataimakinsa, Garba Nadama a matsayin gwamnan jihar, har zuwa watan Nuwamba 1983 da Muhammadu Buhari ya yi juyin mulki da karfin soji.
2- Mamman Bello Ali:
Gwamnan Yobe da ya rasu ne a shekarar 2009 a sakamakon cutar Leukemia, sakanarar bargo.
Gwamna Mamman Bello Ali ya rasu ne a zangon farkon mulkinsa na farko a kasar Amurka, inda yake duba lafiyarsa.
Bayan nan ne aka rantsar da mataimakinsa, Ibrahim Geidam a matsayin sabon gwamnan jihar.
3- Patrick Ibrahim Yakowa:
Gwamnan Kaduna da ya rasu a zangon farko na mulkinsa a 2012 a hasarin jirgin sama, bayan shekara biyu da ransar da shi.
Likkafar Yakowa wanda mataimakin gwamnan Kaduna ne ta daga ne ne bayan Gwamna Muhammad Namadi Sambo ya samu daukaka zuwa mataimakin shugaban kasa bayan Goodluck Jonathan ya gaji kujerar shugaban kasa Umaru Musa Yar’Aduwa, wanda ya rasu a sakamakon rashin lafiya.
Yakowa ya gamu da ajalinsa ne a hanarsa ta Fatakwal daga Jihar Baelsa inda suka halarci jana’izar mahaifin Oronto Douglas.
Helikwaftan da suke ciki tare da tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Janar Andrew Owo Azazi ne ya yi hatsari kuma babu wanda ya tsira.
A cikin jirgin akwi hadimansa guda biyu Dauda Tsoho da Mohammed Kamal da kuma mauka jirgin biyu Murtala Mohammed Daba da Adeyemi Sowole.
Bayan nan ne aka rantsar da mataimakinsa, Mukhtar Ramalan Yero.
4- Rotimi Akeredolu:
Gwamnan Ondo da ya rasu ranar 27 ga Disamamba, 2023 sakamkon rashin lafiya a zango na biyu na mulkinsa.
Rashin lafiyar ta sa shi mika ragamar jihar ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa na kusan wata shida, tun daga lokacin da ya je duba lafiyarsa a kasar Jamus a watan Yuni.