Gwamnonin jihohin Kudu sun yi taron neman haɗin kai a Legas
A Litinin da ta gabata ce ɗaukacin gwamnonin jihohin Kurmi 17 suka yi taro a Legas, inda gwamnan Legas Akinwumi Ambode da takwaransa na Akwa-Ibom Emmanuel Udom suka kasance masu masaukin baƙi, inda taron ya maida hankali a kan ci gaban da yankin Kudancin ƙasar zai samu muddin aka samu kyakkyawan haɗin kai a tsakanin […]
A Litinin da ta gabata ce ɗaukacin gwamnonin jihohin Kurmi 17 suka yi taro a Legas, inda gwamnan Legas Akinwumi Ambode da takwaransa na Akwa-Ibom Emmanuel Udom suka kasance masu masaukin baƙi, inda taron ya maida hankali a kan ci gaban da yankin Kudancin ƙasar zai samu muddin aka samu kyakkyawan haɗin kai a tsakanin jihohin 17.
A jawabin da ya fitar game da taron, Sakataren Gwamnatin Jihar Legas, Tunji Bello ya shaida cewa tun a shekarar 2005 kowace jiha a Kudancin ƙasar nan ke sama wa kanta abubuwan ci gabanta, waɗanda in an kula da su za su yi tasiri wajen samar wa jihohin alfanu da dama. Ya ce taro ne da zai bai wa gwamnonin damar tattaunawa a kan ƙalubalen tsaro a yankin, waɗanda suka haɗa da fashi da makami da garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa da lamuran da suka shafi daidaiton ikon mulki; waɗanda a baya-bayan nan aka maida hankali a kansu a ƙasar baki ɗaya. Ya ce idan aka sami daidaito, ta yadda ɗaukacin jihohin Kudun za su rikaa yin magana da yawu guda hakan ba ƙaramin tasiri zai yi ba.
Taron ya gudana ne bayan shekara 12 da yin irinsa a lokacin Gwamnatin Asiwaju Ahmad Bola Tinubu a Legas a shekarar 2001.