Gwamnonin Kaduna 20 da suka yi zamani da marigayi Sarkin Zazzau
A ranar Lahadi 20 ga Satumba ne Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya koma ga Mahaliccinsa, bayan ya shafe fiye da shekara 45 a gadon sarauta. Marigayi Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84 a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna bayan fama da rashin lafiya. Sarkin Zazzau: Za a yi zaman […]
A ranar Lahadi 20 ga Satumba ne Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya koma ga Mahaliccinsa, bayan ya shafe fiye da shekara 45 a gadon sarauta.
Marigayi Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84 a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna bayan fama da rashin lafiya.
Yana daya daga cikin sarakuna mafiya dadewa a kan karaga, inda a watan Fabrairun da ya gabata ya yi bikin cika shekara 45 yana mulki.
Aminiya ta tattaro muku jerin sunayen gwamnonin Jihar Kaduna da suka yi zamani da Marigayi Sarki Shehu Idris, tun daga lokacin da ya haye gadon sarauta a shekarar 1975 har zuwa mutuwarsa.
Ga jerin sunayen gwamnonin da lokacin da suka shafe a mulki tare da marigayi Shehu Idris:
- Abba Kyari (1967 – 1975) – Abba Kyari ya yi wata biyar kacal ne da marigayin kafin saukarsa daga kujera
- Usman Jibrin (1975 – 1977)
- Mukhtar Muhammed (1977 – 1978)
- Ibrahim Mahmud Alfa (1978 – 1979)
- Abdulkadir Balarabe Musa (1979 – 1981)
- Abba Musa Rimi (1981 – 1983)
- Lawal Kaita (1983)
- Usman Mu’azu (1984 – 1985)
- Abubakar Dangiwa Umar (1985 – 1988)
- Abdullahi Sarki Muktar (1988 – 1990)
- Abubakar Tanko Ayuba (1990 – 1992)
- Muhammad Dabo Lere (1992 – 1993)
- Lawal Jafaru Isah (1993 – 1996)
- Hameed Ibarhim Ali (1996 – 1998)
- Umar Farouk Ahmed (1998 – 1999)
- Ahmed Muhammad Makarfi (1999 – 2007)
- Muhammad Namadi Sambo (2007 – 2010)
- Patrick Ibrahim Yakowa (2010 – 2012)
- Mukhtar Ramalan Yero (2012 – 2015)
- Nasir Ahmed El-Rufai (2015 zuwa yau)