Gwamnonin PDP sun gana don warware matsalolin jam’iyyar

Gwamnonin sun tattauna manyan matsaloli da suka addabi jam’iyyar.

Gwamnonin PDP sun gana don warware matsalolin jam’iyyar

Gwamnonin Jam’iyyar PDP, sun gudanar da wani muhimmin taro don nemo bakin zaren warware matsalolin cikin gida da suka addabi jam’iyyar.

Babban batun da suka tattauna shi ne makomar muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, wanda jagorancinsa ya haifar da rabuwar kai a jam’iyyar.

Haka kuma sun tattauna game da taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) mai zuwa, wanda ake sa rab zai kawo mafita kan makomar Damagum da sauran manyan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi jam’iyyar.

Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Bala Mohammed (Bauchi), Siminalayi Fubara (Ribas), Dauda Lawal (Zamfara), Caleb Mutfwang (Filato), da Ademola Adeleke (Osun).

Manyan shugabannin jam’iyyar kamar Damagum, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Adolphus Wabara, Sakataren Jam’iyya na Ƙasa Samuel Anyanwu, Ma’aji na Ƙasa, Ahmed Yayari Muhammed, da mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba.

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, ya bayyana cewa taron ba na Gwamnonin PDP ba ne, face taro ne na magance matsalolin cikin gida da suka addabi jam’iyyar.

Ya yi alƙawarin cewa za su bayyana matsayar da suka cimma a yayin taron.

Gwamnonin PDP sun musanta ai ƙara a Zamfara

Kazalika, Ƙungiyar Gwamnonin PDP ta ƙaryata rahoton cewa Gwamna Bala Mohammed ko magoya bayansa sun kai ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, don tilasta yin taron kwamitin zarstawa na ƙasa.

Daraktan ƙungiyar, Dokta Emmanuel Agbo, ya ce labarin ba gaskiya ba ne, inda ya buƙaci jama’a su yi watsi da shi.