Gwamnonin PDP sun koka kan ɗage babban taron jam’iyyar

A gefe guda gwamnonin PDP sun buƙaci Tinubu ya sake duba manufofinsa, domin rage wa ‘yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta.

Gwamnonin PDP sun koka kan ɗage babban taron jam’iyyar

Gwamnonin Jam’iyyar PDP, sun buƙaci Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC), ƙarƙashin jagorancin Umar Damagum, da su shiya taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) kafin watan Fabrairun 2025.

Taron dai an daɗe ana ɗage shi tun watan Agusta, duk da cewa ana bukatar shirya shi don tattauna matsalolin jam’iyyar da kuma naɗa sabon shugabanta, wanda zai maye gurbin Iyorchia Ayu da aka dakatar.

Da yake jawabi bayan taron gwamnonin, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, ya ce suna da niyyar haɗa kan jam’iyyar.

Sun amince da ɗage taron NEC na ranar 28 ga Nuwamba domin girmama Gwamna Umo Eno, wanda za a birne matarsa a wannan rana.

Duk da haka, sun jaddada cewa tilas a yi taron NEC a watan Fabrairu don magance matsalolin shugabanci da sauransu da suka addabi jam’iyyar.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan wahalhalun tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC.

Har ila yau, buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sake duba manufofin tattalin arziƙi don inganta jin daɗin al’umma.

Hakazalika, sun soki hukuncin kotu kan nasarar APC a zaɓukan gwamna na jihohin Edo da Ondo.

Gwamnonin sun kuma yi alƙawarin mayar da hankali kan rage wahalhalu da bunƙasa ci gaba a jihohin da PDP ke mulki.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe