Gwanjon gwangwajewar ganyen gaye

Dan gaye Yai ado da ganye Ga shi kamar ya waye Amma kwanya ta juye Wajen laluben Hauro a tsaye   An jinka wa wasu kayan maye A jinka musu ladar tawaye La’adar alaye An maishe su dolaye Suna ahayye nanaye   Miyagu na ta kewaye-kewaye Gayu na ta zagaye-zagaye Da kudi ake muku kaye […]

Gwanjon gwangwajewar ganyen gaye

Dan gaye

Yai ado da ganye

Ga shi kamar ya waye

Amma kwanya ta juye

Wajen laluben Hauro a tsaye

 

An jinka wa wasu kayan maye

A jinka musu ladar tawaye

La’adar alaye

An maishe su dolaye

Suna ahayye nanaye

 

Miyagu na ta kewaye-kewaye

Gayu na ta zagaye-zagaye

Da kudi ake muku kaye

Ko’ina sun mamaye

Sun sayi kuri’a sun boye

 

Tsautsayin tsaye-tsaye

Tsilla-tsillar tusuntsaye

Tsamin tsamiyar tsinkaye

Tanderun tandar toye-toye

Takurar takun tagwaye

 

Cinikin kuri’u

Ya rudar da mutane

Batu ne sananne

A bar batun wane da wane

Mummuna a kawar lu’u-lu’u

 

Ranar sili da zagaye

Mummunar ta’ada ta zuganye

Illolinta an yaye

Masana sun yi kiranye

Sun ce mu daina jaye-jaye

 

Watan Noman-Baba

Takatsantan da romon jaba

Bikin dare guda an caba

tunkarar juna da wuka a daba

Mui wa mutunci haba-haba

 

Shekarar silin madambaci

An hana ha’inci

A kiyayi yi wa juna habaici

Cinikin kudi ya baci

Dabarbarun jefa al’umma a kunci

 

Babban Bakin Ce-ce-ku-ce

Tsaba da tsakuwa a tantance

Bambamin bambance-bambance

matsabbai sun sa an susuce

wayar da ka ne a fakaice

 

A ranar sili da zagaye ga watan Noma-Baba na shekarar dubu karamin lauje da sili da madambaci, BAMBAMIN BATUTUWAN BABBAN BAKIN CE-CE-KUCEN Lantsandan ya shirya shirin ankararwa kan munin  cinikin kuri’u, al’amarin da suka yi nuni da cewa zai iya haifar da zazzabin zabuka a shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa da ke karatowa. Illa dai mafi muni ita ce, cefanar da kasa ga jigari-jigarin jagoran jan ragamar rugurguza zamantakewa da tattali da siyasa.

Dimbin masana daga jam’in jama’ar jami’ar  Mai martaba na Birnin Dabo suka halarci wannan gangami, inda suka nusar da al’umma muhimmancin bin doka. Sannan masu fafutikar damo-da-kura-da-diyya a karkashin tutocin jam’iyyun dan boto da sanda jirge, da tsintsiyar kwakwa da ta laushi ba tare da tsiya-tsiya ba, sun hallara, inda suka nusar da gama-garin mutane yadda ya dace a kada kuri’u.Kuma wani tsohon dan NEHU, dattijon da ya san Aminin siyasar Kanawan Dabo, wato AbdulKarimu Dayyabu ya tabbatar da cewa Malam Nagidan Mambayya ya hana karbar NA-AHU, musamman a wajen takarar zaben wanda duk zai bai wa al’umma kyakkyawan wakilci, don zama ja-gaban jan ragamar jagoranci managarci.

Kodayake dai wani garjejen gaye, wanda ya yi nuni da cewa kansa ya waye daidai lokacin da gari ya waye, a da ana ba su ’yan matsabbai, su bi farfajiyar gidajen al’umma su nunke su a baibai.

Irin wannan tabargaza ta cinikiyyar masu kada kuri’u a kakar kasurarta, Malam Na-kwaciri ya bayyana mana cewa, masu fuka-fukin tashi a birnin Dabo, har GWANJON GWANGWAJEWAR GANYEN GAYE suke yi, domin wanda duk ke da muradi sai ya taya, in aka sallama shi ke nan an yi GA WURI, GA WAINA . Sai dai wani hanzari ba rarewa a guje ba, masanan da Babban- Bakin Ce-ce-ku-ce ya gayyato sun tabbatar wa mahalarta taron cewa,’ LADA DA LA’ADAR LODIN LAFTUN LALLAGA LUMANA,’ ake auno wa al’umma. Kuma kin amincewa da faruwar GWANJON GWANGWAJEWAR GANYEN GAYE, tamkar inkarin ikrari kan maganar tsari, wato ga waina, ga wuri, inda rashin wuri ke rusa jari ga zuki-ta-malle iri-iri.

Haurobiyawa dai sun saba da walle-wallen wasan Samson-siya-siya da kwakwalwar talakawa da ’yan takara da masu taka karan danni ke tsuwurwurtawa. Domin tsawon mulkin mulaka’u na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, wanda aka shafe shekaru sili da manuniyar sama ana fama, ba wani abin ta’ajibi ba ne a hango wadanda suka yi ado da ganyayyaki a kan layin kada kuri’a. Shi ya sa ma nake ganin magabtan al’umma sun yunkuro da ’yan matsabbai don su nunke jama’a a baibai.

’Yan makarantar Dodorido da ke koyon falle shafukan mujallu da makalu da wagagen litattafai a farfajiyar wannan makaranta da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, lokaci ya yi da za mu tabbatar da batun Malam Mai yaren Hauhau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, cewa: Halin mutum jarinsa.” Lallai mu yi karatun ta-natsu, don gudun kada a karke da tsilla-tsillar tsallen badake kamar tsuntsu, wanda kwanyarsa ta motsu. ’Yan makaranta mu natsu, mu daina yi wa juna nunin yatsu, mu himmatu ka’in da na’in wajen ganin kyawawan ta’adu sun hau tudu sun warwatsu.

A nan ya kamata mu fasko cewa duk wanda ke fargabar cafke SAMARIN KUSU DA ’YAN MATAN JABA DA GAFIYA, to shi ne ke kwakwar kundunbalar kundume kuri’u, sannan jama’ar da hankalinsu yake a hannun taguwa, su ne ke cancancarewa a carin ’ Gwanjon gwangwajewar ganyen gaye.’

Bisa la’kari da shirin da magabta al’umma ke yi na cinikin RA’AYI, don su mayar da shi RAIRAYI, manhajar makarantarmu mara hajijiya za ta ci gaba da baje dabarun bin DOKA don kada kowa ya KOKA, tare da kawar da JUHALA don tabbtar da ADALA, ta yadda daukaci al’umma za su ji dadin yin WALWALA, tare da karsashin rashin KASALA a duk lokacin da suka yi bitar MAKALA, ta yadda cikin sauki za a fasko cewa ba ma TALLA. Kuma wadanda ke cinikin ALALA su ne ke laluben GALALA don dinka galleliyar GALILA, ta yadda za su  ji dadin sanya gama-garinal’umma su yi tadundume kururu da GAJALA.