Gwano ba ya jin warin jikinsa sai na wani
A rayuwa babu mahalukin da ke son zamantowa santolabi, mara wani amfani kamar holoko hadarin Kaka, wanda ke wucewa bai zubo ruwa ba. Zai fi so ya aikata abubuwan da za su amfani jama’arsa, wadanda za a yi ta kwanzartawa sa’ilin yana raye, a kuma yi ta rubutawa bayan rasuwarsa don na baya su yi […]
A rayuwa babu mahalukin da ke son zamantowa santolabi, mara wani amfani kamar holoko hadarin Kaka, wanda ke wucewa bai zubo ruwa ba. Zai fi so ya aikata abubuwan da za su amfani jama’arsa, wadanda za a yi ta kwanzartawa sa’ilin yana raye, a kuma yi ta rubutawa bayan rasuwarsa don na baya su yi ta karantawa. Irin wannan rayuwar ce tsohon shugaban Afrika Ta Kudu, Mista Nelson Rohlilahlah Madiba Mandela ya yi shekaru casa’in da biyar da suka shude. Mista Mandela ya daukaka matsayin Afirka ta Kudu a kasashen duniya, ya kuma samu daukaka shi kansa da mutuntaka a idanun duniya, ya kuma yi carar da aka ji ta a dukkan nahiyoyi da kuma kusurwowin duniyar nan.
A takaice dai ana iya cewa marigayi Mandela ya kasance magajin mazajen farko da suka fara gwagwarmaya da Turawan Mulkin Mallaka a Afirka ta Kudu, shi da jama’arsa kuma sun gamu da tsananin wahala da wulakanci a fafutikarsu ta ci gaba da yakar miyagun manufofin nuna bambancin launin fata da kuma tabbatar da mulki bakaken fata da suka fi rinjaye a kasar haihuwarsu maimakon ‘yan tsirarun jar fatar da suka yi kaka-gida a kasar sakamakon ci-ranin da suka zo yi fiye da shekaru dari uku.
A matsayinsa na matashin lauya, mai tsananin kishin kasarsa da kuma kaunar kyautata wa jama’arsa, Mandela ya yi gwa-gwa-gwa da makiyan kasarsa da al’ummomin cikinta; ya kuma nuna tsananin bajinta da juriya da hakuri sa’ilin da aka garkame shi har na tsawon shekaru 27 a gidan jarun; ya kuma shimfida adalci, ya kuma kamanta gaskiya sa’ilin da ya mulki kasar bayan janyewar Turawan da suka kuntata wa kasarsa, ya kawo sabon yanayin da ya tabbatar da ‘yanci da daidato tsakanin dukkan kabilun kasar, bakake da fararen fata.
Babu shakka wadannan kyawawan halaye da dabi’u da suka wajaba ne a samu game da dukkan mutumin da zai yi fice a harkokin siyasa da na mulkin jama’arsa. Hakika, kasar Afirka ta amfana daga gwagwarmayar da Mandela da mutanensa suka yi, kafin shigarsa kurkuku da kuma yayin da yake gidan jarun, inda ya ci gaba da tuntubar jama’arsa a asirce, suna tsara hanyoyi da dabarun ci gaba da gwagwarmayar kwatar ‘yanci.
A daidai wannan lokacin ne kuma wasu muhimman kasashe a yankin Afrika ta Kudu suke fadi-tashin neman ‘yancin da Turawa suka danne musu bayan takwarorinsu da yawan gaske na nahiyar Afirka sun zame ‘yantattu.
Gwagwarmayar irin wadannan kasashen ya fito fili ne kuwa a karkashin jagorancin Najeriya, sa’ilin da ta dukufa wajen kwato wa Afrika ta Kudu da sauran ‘yan uwanta na Kudancin Afrika ‘yanci, kuma gudummawar da shugabannin Najeriya suka bayar game da haka ba ta misaltuwa, ta kuma biya dukkan bukatar da ake so dangane da haka. Amma da yake duniya ba ta da gaskiya, sai ga shi nan Shugaba Goodluck Jonathan ya yage wagegen bakinsa, yana cewa cikin shugabannin Najeriya kafatan, babu wanda ya kai Mandela a daraja ko wajen kyautata wa jama’arsa, domin kuwa sun fi gwanancewa ne wajen takura wa jama’arsu, sun kuma hana su shakar iskar ‘yanci, sa’anan suka kuntata rayuwarsu, suka hana musu rawar gaban hantsi.
Haka nan kuma, yayin da yake jawabi a wajen ta’aziyyar Nelson Mandela a mujami’ar da ke fadarsa a Abuja, Dokta Jonathan ya soki lamirin ‘yan siyasar kasar nan wadanda ya ce iyayen gidansu sun cika dagawa, sun kuma dauki kawunansu tamkar dagutu ko mamallakan jama’ar da suke tare da su, kuma a cewarsa hakan bai dace ba, da kyawawan halayen da suka sanya ake kwanzarta marigayi Mandela a duk fadin duniyar nan. To ai ba wanda zai yi mamaki idan Shugaba Jonathan ya fadi haka, domin kuwa wanda duk bai san ciwon kansa ne ba ke yin kirari, ya daba wa cikinsa wuka. Shugabannin Najeriya, musamman ma, na jamhuriya ta farko sun yi kyakkyawar shimfidar da shugabannin gwamnatin sojoji suka yi amfani da ita don ‘yantar da kasashen Afrikan da suka makale cikin kangin bauta domin ta haka ne kawai kasarsu ita ma za ta iya tsira da mutuncinta.
Kuma da wane dalili ne Shugaba Jonathan zai iya furta irin wadannan kalamun, alhali kuwa ko na goye na sane da cewa saboda lusaranci babu wani abin da gwamnatinsa ke tsinana wa wajen agazawa kasashen Afirka da ke fama da matsalolin zamani wadanda suke barazar kai su kasa. Ta haka ne shi ma ya kasance tamkar sauran shugabannin kasashen Afirkan da suka shantake, suna biye wa Turawan da ke tatike arzikin kasarsu karkaf, suna kuma hure masu kunne don su dawwama bisa mulki, suna cewa Allah Ya maimaita, jama’arsu kuwa na fatan Allah Ya yaye masu su.
Wai shin a yanzu Shugaba Jonathan na da bakin magana ganin cewa a duk fadin Afirka kasarsa ce ke kan gaba daga cikin wadannda ba su zaman lafiya saboda fitintinun da rashin adalci ya haddasa, sa’annan kuma rikice-riken addini da na kabilanci sun dabaibaye ta, ta kasa gusawa gaba? Ai inda shi da manyan jami’ansa suka fi auki shi ne wajen tallabar rashawa da yin sakaci wajen hukunta jami’an gwamnatinsa da manyan ‘yan jam’iyyarsa wadada suka zarme a wannan fannin.
Shugaba Jonathan ya yaba da rayuwar Mandela ta rashin son kai da biye zuciya, ya kuma ce wannan ne ya sa a yanzu wadanda a zamanin da yake gwagwarmaya da su, har suke kiransa dan ta’adda, suka komo suna kwarzanta shi. Ashe ke nan abin da ya ba ka tsoro wata ran zai komo ya ba ka tausayi. Hakan ake fata Shugaba Jonathan da sauran jama’arsa su yi nan gaba, watau su gane gaskiya, su kuma yi aiki da ita wajen wanke wadanda suka yi wa zargin ta’addanci na babu-gairan-babu dalili, su kuma komo su nemi gafara daga gare su. Amma hakan zai yi wuya a gare su, domin idanuwansu sun dode, hankulansu sun gushe, babu abin da ke zuciyarsu sai zargin abokan zamansu game da ta’asar da su ne kan gaba wajen aikatawa domin kuwa an ce gwano bai jin warin jikinsa sai na wani.