Gwarazan Shekara 12 da na zava
Wadannan su ne gwarazana na shekarar 2018. Duk wanda kuka gani na zayyano shi, ba wai don ya fi kowa cancanta ba ne, kuma ba wai babu wani mai yin alherin da ya kai nasa ba ne, ko ya fi nasa, a’a na yi amfani ne da iya abin da na sani ne game da […]
Wadannan su ne gwarazana na shekarar 2018. Duk wanda kuka gani na zayyano shi, ba wai don ya fi kowa cancanta ba ne, kuma ba wai babu wani mai yin alherin da ya kai nasa ba ne, ko ya fi nasa, a’a na yi amfani ne da iya abin da na sani ne game da mutum. Kowanne daga cikinsu za ku ga na dan bayyana wani alherinsa kadan.
- Shugaban Kasa Buhari: wannan bawan Allah ko ban ce komai a kansa ba jin sunansa ma kadai ya wadatar. Domin duk wani mai ji ko gani a kasar nan ya san wane ne shi da irin abubuwan alherin da yake yi wa kasarsa. Baba Buhari shugaba ne da muka yi imani ba azzalumi ba ne, kuma ba zai zalunce mu ba, ba zai kuma bari a zalunce mu ba, iya iyakar iyawarsa. Ya karbi mulkin Najeriya a lokacin da take a hargitse, take fama da matsaloli barkatai. Baba Buhari an zabe shi ne a matsayin gwarzon shekara sakamakon ba da himma wajen samar da tsaro a kasarmu da yaki da cin hanci da yaki da satar mutane domin neman kudin fansa da magance matsalar fasa bututun man fetir, uwa uba da yadda gwamnati ke kokari a kullum wajen samar wa matasa aikin yi da kuma samar da tsare-tsare da dama na ba da tallafin sana’a da noma. Shirin N-Power da ciyar da dalibai ’yan firmare kadai idan aka ambata sun wadatar a kira Baba Buhari a matsayin gwarzon shekara.
- Muhammad Babandede: Shi ne Shugaban Hukumar Shige da Fice wato ‘Immigration.’ Mutum ne wanda alherinsa ya bazu ciki da wajen jiharsa ta Jigawa. Kazalika yana yi wa kasarsa aiki tukuru ba dare ba rana. Akwai dimbin mutane da dama da suka samu aikin Immigration ta silarsa. Tun kafin ya zama shugaban hukumar a bangaren aikinsa tsawon shekaru da suka gabata alherinsa ya fasu. A kwanan nan ta dalilin jajircewarsa da nuna kishi ga talaka, Babban Asibitin Hadeja ya samu kayan aiki na zamani inda zai yi gogayya da asibitocin da suka sha gabansa a wajen kayan aikin jinya na zamani.
- Alhaji Ubali Gwanki Guri: Matashi ne yana harkar sayar da dabbobi, shi ne kuma Sarkin Kasuwa ya gaji mahaifinsa wanda Allah Ya yi masa rasuwa a bara. Akwai mutane da dama da suke amfana da shi, wadanda suka hada da ’yan uwa da ’yan unguwa da yankin da yake. Shi ne wanda ya dauki alkawarin daukar nauyin karatun wani yaro da ya Musulunta daga makarantar sakandare har ya gama jami’a. Sannan ya dauki alkawarin ba shi gida idan lokacin aurensa ya yi tare da ba shi jarin sana’a. A gaskiya wannan mutum mai yi ne yana da kyautatawa sosai.
- Alhaji Baffa Inusa Abdulkadir (Kabon Hadeja): Ya kasance basarake mai kishin al’ummarsa da son ci gaban garinsa. Haka zalika ya kasance daya daga cikin masoya Baba Buhari na gaske. Ya na kuma dauke da akidu irin na Baba Buhari na son ganin an gyara kasa. Baya da haka yana taimakon al’umma daidai gwargwado ta fuskoki da dama.
- Aliyu Abdullahi: Ma’aikaci a Sashin Hausa na gidan rediyon Jamus wato (DW Hausa). Aliyu mutum ne da kullum kwarewarsa a aiki take bayyana. Na zabe shi a matsayin daya daga cikin gwarazan shekara bisa dalilai da dama ga wasu daga ciki: Shi ne jagoran shirin wasiku na ra’ayin matasa da ake gudanarwa a tashar DW Hausa a duk tsakiyar mako. Shiri ne da kullum yake kayatar da masu sauraro. Baya ga haka a sauran kwanakin mako akwai ranakun da a nan ma yakan jagoranci shirin karanta wasiku, wanda a nan ma kwarewarsa tana bayyana da kuma gogewa a aikin jarida. Yakan zakulo wasiku masu muhimmanci ga al’umma ya karanta, game da abin da ya shafi koke-koke ko korafi ko yabo ga wani ko wata ko ga gwamnati a bisa wani abin alheri.
- Alhaji Salisu Zakar Hadeja: Shugaban Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Jigawa (SUBEB). Ya kasance a cikin gwarazana ne saboda kokarin da yake wajen jajurcewar ganin ilimi ya inganta. Mutum ne jajurtacce, mai son kyautatawa al’umma. Rike hukumar SUBEB da ya yi an sami sauye-sauye da dama masu muhimmanci.
- Ibrahim Alhaji Bako Guri: Dan kasuwa ne, duk da ba za mu sa shi sahun attajirai ba. Yana da shagon magunguna wato Kemis a cikin garin Guri, yana kuma da sauki a harkar kasuwancinsa, bisa wannan dalilin nake ga ya kamata ya shigo cikin jerin gwarazan da na zakulo. Shi ne gwarzon dan kasuwa na Kungiyar Muryar Talaka ta Shekarar 2018.
- Dokta Nuruddeen Muhammad Hadeja: Tsohon Minista a gwamnatin Shugaba Jonathan. Wannan bawan Allah abu daya kawai na kalla na ga ya dace ya kasance daga cikin jerin gwarazan da na zakulo, wato samar da gidan rediyo mai zaman kansa da ya yi mai suna SAWABA FM a cikin garin Hadeja. Abin da al’ummar yankin suka jima suna nema tsawon lokaci.
- Alhaji Malam Daihuru Guri: Yana harkar kayan gine-gine da harkar sayar da filaye bashi da matsaa da kowa daidai gwargwado. Yana kuma kyautatawa a tsakaninsa da mutane, ta fuskar kasuwancinsa. Akwai bukatar sauran masu sana’a irin tasa su kasance masu koyi da halayensa.
- Ibrahim Hassan: Mataimakin Gwamnan Jigawa. Yana da dabi’u da dama da suka sa ya sha bamban da ’yan siyasa da dama, wajen kamanta gaskiya da rike amana. A baya kafin wannan lokacin ya rike mukamin Kwamishina da Sakataren Jiha, ya yi Mataimakin Gwamna, amma ba mu ji wani lokaci da aka bayyana shi a matsayin wanda ke da tabon cin hanci da rashawa ba. Baya ga haka mutum ne kaifi daya kuma mai son gina dan Adam. Yana daukar nauyin jinya na mutane tsawon shekaru. A takaice mutum ne na mutane mai taimako sosai. Yana kuma daya daga cikin gwarazan shekarar 2018 na Kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Jigawa.
- Injiniya Magaji Da’u Aliyu: Dan Majalissar Wakilai ne, mai wakiltar Buji da Birnin Kudu. Yana da ofishi wanda a karkashin ofishin akwai ma’aikata da yake biyansu albashi. Ya kama dakunan kwana ga dalibai da ke karatu a ciki da wajen Jihar Jigawa ’yan mazabarsa, sannan yana ba da tallafin karatu ga dalibai. Yana kuma raba fom din jarrabawar JAMB. Ya sama wa matasa da dama aikin gwamnati. Ko a kwanaki kadan akwai mutane sama da 20 da ya samawa aikin gwamnati. Injniya Magaji Da’u Aliyu shi ne ya lashe zaben gwarzon shekara, na dan siyasar da ya fi kyautata wa al’ummarsa na Kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Jigawa na 2017 da na 2018. Sau biyu ke nan kungiyar tana karrama shi a jere.
- Datti Assalafy: Wannan ina abota da shi ne a shafin facebook, yana kuma daga cikin mutanen da suke kan ganiyarsu a fagen rubuce-rubuce a shafin, musamman wadanda nake abota da su. Yana da tarin mabiya masu yawan gaske, wadanda suke karanta rubutunsa. Kuma dan kishin kasa ne. Yana rubutu sosai masu ma’ana. Da wahalar gaske ka ga ya rubuta wani abu wanda bai dace ba, mutane na jin dadi da kuma amfana a rubutunsa. Ya bambanta da marubuta da dama a shafukan sada zumunta.
Aikin alheri ko yaya yake idan ka aikata shi al’umma na ankare da kai, kuma labarinka zai kai inda ba ka tsammani. Kamar yadda mutum idan yana abin tsiya nan ma ana ankare da shi kuma labari zai je inda bai zato ko tsammani.
Alaka ta kusa ko ta nesa mafi yawansu ba ni da ita da su. Kashi biyu cikin uku ko ganinsu ban taba yi ba, amma ina da masaniyar alherinsu kamar yadda na bayyana a takaice. Allah Ya sa wata rana mu ma mu yi abin da za a yaba mana, muna raye ko kuma bayan mun bar duniya.
Daga Nasiru Kainuwa Hadeja
(Shugaban Kungiyar Hantsi Youth Organization) 08100229688/09073801967.