Gwargwadon gudunmawarka, gwargwadon abincinka —Ango da amarya
Gudummawa mai yawa daidai da abinci mai kyau.
Bikin aure na cikin mafiya muhimman biki a rayuwar ango da amarya.
Kuma akan yi shirye-shirye sosai don faranta wa bakin da za su halarci bikin auren don su sa albarka ga ango da amaryar.
Sai dai wani ango da amaryarsa sun bullo da wani sabon salo inda suka rarraba wa bakin takardu kan su fadi kyautar da suka kawo don tsara irin abincin da za a ba su a yayin bikin.
Takardar tana dauke da kanun “Kudi mai yawa daidai da abinci mai kyau?”
Takardar ta nuna an rarraba bakin zuwa aji hudu da suka kunshi, ‘kyautar soyayya da kyautar zinare da kyautar azurfa da kyautar lu’u-lu’u.”
Idan bakin sun bayar da abin da ya kai Dala 250 suna ajin ‘kyautar soyayya’ da za a ba su naman gasasshiyar kaza da kifi.
Idan kuma kyautar ta kai Dala 251-500 ta fada ajin ‘kyautar azurfa’ da za a iya ba su abincin da ya gabata tare da zabin karin makulashe.
Sannan idan bakin suka bayar da Dala 501-1000 sun fada ajin ‘zinare’ inda za a ba su abinci mafi tsada kan na baya.
Wadanda kuma suka ba da Dala 1000-2500, suka fada ajin ‘lu’u-lu’u’ suke da zabin kasancewa a ajin farko ko na biyu ko na uku tare da samun jaka dauke da kyautar giyar nan ta Champagne.
Wannan lamari dai ya faru ne a kasar Indiya.