Gwarzon Afirka na Daily Trust ya karbi kyauta
Wani dan kasar Ghana mai shekara 34 mai suna Mutaru Mumuni Mukthar, ya karbi lambar yabonsa a matsayinsa na Gwarzon Afirka na jaridar Daily Trust na bara. Kuma ya karbi kyautar Dala dubu 25 (kimanin Naira miliyan tara) da Bankin UBA yake daukar nauyin bayarwa. Mukthar, wanda aka mika masa kyautar a wajen liyafar cin […]

Wani dan kasar Ghana mai shekara 34 mai suna Mutaru Mumuni Mukthar, ya karbi lambar yabonsa a matsayinsa na Gwarzon Afirka na jaridar Daily Trust na bara.
Kuma ya karbi kyautar Dala dubu 25 (kimanin Naira miliyan tara) da Bankin UBA yake daukar nauyin bayarwa.
Mukthar, wanda aka mika masa kyautar a wajen liyafar cin abincin dare a shekaranjiya Laraba a Abuja, an zabe shi ne sakamakon kyakkyawan misalin da ya nuna wajen yaki da ta’addanci inda hakan ya jawo ya sauya ra’ayin wadansu da ke kokarin zama masu tsattsauran ra’ayi a Afirka.
Shi ne dan Afirka mafi karancin shekaru da ya taba cin wannan lambar yabo.
Sannan an bai wa wani Farfesa dan kasar Masara, Farfesa Magdi Habib Yacoub lambar yabo ta samun Nasara a Rayuwa domin cika shekara 10 da bullo da shirin Gwarzon Afirkan.
Likitan mai shekara 82 an karrama shi ne kan rawar da ya taka a sassan duniya da kuma ayyukansa na jin kai da kyawawan misalan da ya bayar wajen gudanar da tiyatar zuciya ga yara a sassan Afirka.
Jakadan Masar a Najeriya Mista Assem Mohammed Hanafi ne ya karbi kyautar a madadin Farfesa Yacoub wanda bai samu halarta ba.
Wani lauya dan Najeriya, Barista Zannah Mustapha wanda yake taka rawa wajen kula da yaran da rikicin Boko Haram ya mayar marayu yana daga cikin wadanda suka fafata a gasar.
Shugaban kwamitin alkalan bayar da lambar yabon, kuma tsohon Shugaban kasar Botswana Mista Festus Mogae, ya ce an zabi Mukthar Gwarzon Afirka na shekarar 2017 ne bayan an gudanar da gagarumar daddaleawa.
“Wajibi ne mu fahimci cewa akwai talakawan Afirka da dama da suke bayar da gagarumar gudunmawa da sadaukar da rai domin amfnin mutane a sassan Afirka. Wannan lambar yabo za ta ci gaba da tsakulo mutanen da suke ayyukan kirki da za su zamo ababen koyi ga sauran jama’a,” inji shi.
Ya ce, Afirka tana bukatar masu bayar da misalai don haka shirin Gwarzon Afirka ya zo ne domin gano tare da karrama talakawan da suke yi ayyuka ababen misali.
Ya yaba wa Bankin UBA kan daukar nauyin bayar da kyautar kudin da ke tare da lambar yabon inda ya bukaci sauran kamfanoni su tallafa wa shirin.
“Shirin Gwarzon Afirka babban shiri ne da yake kokarin canja labaran da ake bayarwa a kan Nahiyar Afirka. Shirin a kashin kansa yana bukatar tallafin kamfanoni musamman wadanda suka yi imani da matsayin Afirka kuma suke son daukaka nahiyar,” inji shi.
A jawabin Daraktan Gidauniyar MacArthur kuma Shugaban taron, Dokta Kole Shettima, ya ce, duniya ba ta samun damar jin abubuwan da ’yan Afirka suke yi domin inganta rayuwar mutanen Afirka. “A Afirka kullum muna magana ne a kan matsaloli kamar yunwa da fari da yakin basasa. Wannan babban tarnaki ne kuma yana shafar rayuwar yaranmu,” inji shi.
Sai ya yaba wa mahukunta Kamfanin Media Trust wadanda suka bullo da shirin bayar da lambar yabon kan bullo da shirin zakulo gwarazan da suka sadaukar da lokaci da karfinsu wajen inganta rayuwar jama’a.
Da yake jawabi bayan karamma shi a Cibiyar Shehu Musa ’Yar’aduwa da ke Abuja, Muntaru Mumuni Mukhtar ya ce lambar yabo ta Gwarzon Afirka na shekarar 2017, za ta kara masa kwarin gwiwa a kokrinsa na yaki da ta’addanci a sassan Afirka.
Ya ce, “Ta’addanci wata barazana ce mai sarkakiya. Kuma yakarsa da hukumomi ke yi da makami kawai ya nuna ba zai samar da nasarar kawar da shi ba. A yayin aikina na fahimci cewa yaki da ta’addanci da akidun tayar da zaune-tsaye ba zai samu ta hanyar fafatawa a fagen daga kadai ba. Za a iya samun nasara ta hanyar sauya tunanin matasan da ake ingizawa da kuma jama’ar da suke yankunan.”
Ya ce a kokarin gudanar da aikinsa ya saurari bayani mai tayar da hankali daga wani matashin da aka ingiza kuma ya yi kokarin tayar da bam a Majalisar Dokokin kasarsa, sakamakon halin damuwa da ya shiga kan labaran da kafafen watsa labarai suke bayarwa game da muguwar almundahanar da ake yi a kasarsa.
Ya ce zai yi amfani da kudin da aka ba shi wajen aikin samar da zaman lafiya da yake yi a sassan Afirka ta Yamma. Sai ya ce ya sadaukar da lambar yabon ga wadanda ayyukan ta’addanci suka rutsa da su, musamman wadanda a rayuwarsu ba su taba tunanin yin amfani da tashin hankali don nuna fushinsu ba.
Wanda aka haife shi a garin Salaga da ke Arewacin Ghana, kuma ya fito daga iyalan kananan manoma, Mutaru ya kafa kuma ya zama Babban Daraktan Cibiyar Yaki da Ta’addancin ta Afirka ta Yamma (WACCE) da ke Ghana.
Ya yi digiri a kan harkokin shugabanci a Jami’ar Asheshi da ke Ghana, kuma a shekarar 2013 ya yi digiri na biyu kan yaki da ta’addanci a duniya da yaki da miyagun laifuffuka da tsaron duniya a Jami’ar Cobentry da ke Ingila.
Rikicin kabilanci a tsakanin Nanumba da Konkomba a 1994 da ya rutsa da danginsa inda aka hallaka mutum dubu da raba dubbai da muhallinsu ne ya karfafa masa gwiwa ya shiga yaki da ta’addanci.
Mukhtar yana aiki a sassan Afirka ta Yamma tare da ayarin kwararru, inda yake tattaunawa da matasan da aka cusa musu tsaurin ra’ayi, kuma ya taimaka musu su sake dawowa cikin jama’a ko makaranta ko su kama aiki.
Manyan mutane da dama sun halarci bikin ciki har da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da tsohon Shugaban Hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da Kakakin Shugaban kasa Garba Shehu da sauransu.