Gwarzon Dan Kwallon Duniya: Yadda nasarar Messi ta jawo muhawara

Messi ya ce Lewandowski ya cancanci kambin Ballon d’Or, a yayin da wasu ke ganin ba Messi ya cancanci kambin na 2021 ba

Gwarzon Dan Kwallon Duniya: Yadda nasarar Messi ta jawo muhawara

Dan wasan Kungiyar PSG da kasar Ajantina, Lionel Messi, ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya na bana.

Wannan ne karo na bakwai da Messi, mai shekara 34 ya lashe kambun, a yayin da Cristiano Ronaldo ke biye masa da guda biyar.

Messi ya lashe kambin na Ballon d’Or a shekarun 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da 2015 da 2019 sai kuma a bana.

Robert Lewandowski na Kungiyar Bayern Munich da kasar Poland ne ya zo na biyu. Shi ne kuma ya samu kambin Gwarzon Dan Wasan Gaba na Duniya, inda ya yi wa Gerd Muller zarra wurin yawan zura kwallaye a kaka daya ta Gasar Bundesliga ta kasar Jamus.

Jorginho na Chelsea da kasar Italiya ne ya zo na uku a jerin ’yan kwallon duniya na bana.

Zababbun ’yan jarida 170 da wasu zababbun masu horar da ’yan wasa da kyaftin-kyaftin ne suka jefa kuri’a a zaben.

Messi ya samu maki 613, sai Lewandowski ke biye masa da maki 580, sai Jorginho ya samu maki 460.

Karim Benzema na Kungiyar Real Madrid da kasar Faransa ne na hudu.

Na biyar kuma N’Golo Kante na Kungiyar Chelsea da Faransa.

Cristiano Ronaldo na kasar Portugal da Kungiyar Manchester United, shi ne ya zo na shida.

Wannan ne karo na farko tun a shekarar 2010 da Ronaldo ya kasance ba ya cikin ukun farko a gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniyar.

Yadda Messi ya lashe kambin

A kakar wasa ta bana, Messi ya lashe Kofin Copa America, inda kuma ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan gasar da kuma wanda ya fi zura kwallaye a gasar.

Sannan ya fi Lewandowski yawan nasarar zarra a wasanni da hada wasa.

Lewandowski ya cancanci Ballon d’Or —Messi

Da yake jawabi bayan karbar kambin, Messi ya ce shi ma Lewandowski ya cancanci a ce ya samu nasarar kambin.

A cewar Messi, “Robert, ka cancanci lashe kambin Ballon d’Or.

“A kakar bara, kowa ya amince kai ne ka cancanci lashe kambin.

“Ina tunanin ya kamata Kungiyar Kwallon Kafa ta Faransa ta ba ka kambinka na Ballon d’Or na bara; Ka cancanci hakan,” inji Messi.

A kakar bara, Lewandowski ne ke kan gaba wajen kowane abu da ake bukata domin lashe gasar, amma sai annobar COVID-19 ta hana bayar da kyautar a barar.

Sai dai kuma Lewandowski ya lashe kambin Gwarzon Dan Wasan Gaba, wanda wannan ne karo na farko da aka bayar da kambin.

Ce-ce-ku-cen da biyo bayan sanar da wanda ya lashe kambin

Sai dai jim kadan bayan sanar da wanda ya lashe kambin, sai aka shiga musayar yawu musamman a kafofin sadarwa a tsakanin masoya Messi da ya lashe kambin da wadanda suke tunanin bai cancanci lashe kambin ba.

Messi da Lewandowski a kakar bara

Messi ya buga wasa 56, inda ya zura kwallo 41, ya taimaka an ci kwallo 17.

Sannan ya lashe Kofin Copa America da Copa del Rey.

Shi kuma Lewandowski a kakar ya ci kwallo 64, ya taimaka a zura kwallo 10, sannan ya lashe Kofin Bundesliga da Club World Cup da DFL-Supercup.

Wannan ne ya sa wadansu suke ganin Lewandowski ne ya cancanci kambin ba Messi ba, yayin da su kuma magoya bayan Messi suke cewa hassada ake masa.

A cewar wani mai sharhi kan wasanni a Kano, Mubarak Abubakar, wanda masoyin Messi ne, ya ce, “Ka koma kallon dambe! Kwallon kafa ta masananta ne, sun fi kowa saninta da dokokinta.

“Duk wanda ba ya da ilimin harkar kuma yake ganin hukuncin da mafi rinjayen masu ruwa-da-tsaki a harkar suka yanke bai masa ba, to fa sai dai ya koma kallon dambe ko kokawa ko langa, tunda ita ya gada iyaye da kakanni, domin ra’ayinsa bogi ne kawai ga duk mai hankali.

“Ko tsarin ’yan wasa a cikin fili goma aka ce ka kawo da inda kowane dan wasa zai tsaya ba za ka iya ba, ballantana ka kawo dokokin zura kwallo a raga da kati da sauran abubuwan da suka wakana game da kowane dan wasa a wannan shekarar ba za ka iya ba;

“Amma ka dage cewa masu ruwa-da-tsaki a harkar ba su iya ba, alhali su suka hadu, mafiya rinjayensu suka yanke hukunci.”

Injiniya Abubakar Suleiman cewa ya yi, “Kasancewa a yanzu Messi ba ya tabuka wani abin a-zo-a-gani, shi da kansa ya san kambin na bana bai cancanta ba; Wannan fashi da makami ne a gasar Ballon d’Or.”

Jaridar Bild ta kasar Jamsu ita ma ta ruwaito a wani rahotonta cewa, “Wannan ba gaskiya ba ne. Akwai cuwacuwa a ciki,” kamar yadda jaridar Mail ta ruwaito.

Da yake jawabi, tsohon dan wasan Jamus, Lothar Mathaus, wanda shi ma ya lashe kambin a1990 ya ce a yanzu bai gane yadda ake bi wajen zaben ba, inda har Lewandowski bai lashe kyautar ba.

“Maganar gaskiya ita ce bayan wannan lashe kambin da Messi ya yi, na shiga rudani game da lamarin.

“Cikin girmamawa ga Messi da sauran wadanda aka zaba, gaskiya babu wanda ya fi Lewandowski cancanta,” kamar yadda ya fada wa jaridar Sky Sports ta Jamus.

Wadansu suna cewa an ba Lewandowski kambin Gwarzon Dan Wasan gaba ne domin a rarrashe shi, wanda da yawa daga cikin magoya bayan Messi suke mayar da martani da cewa ba haka ba ne, Messi ne ya cancanta, hassada kawai ake masa, inda wadansu suke cewa magoya Cristiano Ronaldo ne suke goyon bayan Lewandowski domin kyashi ga Messi.

A bangaren mata, ’yar wasan Spain da Barcelona, Aledia Putellas ce ta lashe kambin Gwarzuwar ’Yar Wasan Duniya.

Golan PSG da Italiya, Gianluigi Donnarumma ya zama Gwarzon Gola.

Sai dan wasan Barcelona da Spain, Pedri ya lashe Gwarzon Matashin Dan Kwallo.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara