Gwarzon Sojan Sama Bashir Umar
Yadda ake samun karancin wadanda za a karrama don wata bajinta a tsakanin al’ummar Najeriya, wannan ya sa labarin Sojan Saman Najeriya Bashir Umar, wanda ya tsinci makudan kudi kuma ya mayar wa mai shi, bayan ya tsinci kunshin kudin kasar waje a Kasuwar Sansanin Alhazai da ke Kano a ranar 16 ga Yuli ya […]
Yadda ake samun karancin wadanda za a karrama don wata bajinta a tsakanin al’ummar Najeriya, wannan ya sa labarin Sojan Saman Najeriya Bashir Umar, wanda ya tsinci makudan kudi kuma ya mayar wa mai shi, bayan ya tsinci kunshin kudin kasar waje a Kasuwar Sansanin Alhazai da ke Kano a ranar 16 ga Yuli ya cancanci a taya shi murna. Bashir dan shekara 24 ya dawo da kudin da ya kai kimanin Naira miliyan 14 da dubu 843 da 300 ga mai shi, a wannan mawuyacin halin matsi da ake ciki a kasar nan.
Mayar da kudin da Umar ya yi ga mamallakin kudin ba tare da wata tirjiya ba ya nuna cewa duk lalacewa a cikin al’umma ba a rasa na kirki, musamman cikin matasan wannan lokaci.
Umar ya kasance ma’aikaci ne a Rundunar Sojin Saman Najeriya a wata rundunar tafi-da-gidanka da aka samar da ita don samar da tsaro a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Ya tsinci kunshin kudin ne lokacin da suke bakin aiki tare da abokan aikinsa.
Sojan ya dawo da kudin ne bayan da ya ga wata lambar waya a cikin kunshin kudin sai ya kira mai kudin Alhaji Ahmad kana ya damka masa kudinsa.
Gamsuwa da irin amana da halin kirki da wannan matashi ya nuna ya sa Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya Iya Mashal Sadik Abubakar ya karrama wannan soja a wata liyafa ta musamman da aka shirya a Hedkwatar Sojin Sama da ke Abuja a ranar 25 gaYuli. Ya ce Umar ya nuna bajinta da gaskiya wajen maido da kudin ga mai shi.
Ya ce Umar ya sake fito da martabar Rundunar Sojin Sama wacce dama aka san rundunar da ita. Daga nan sai Shugaban Sojin Saman ya kara wa Umar mukami biyu inda aka maida shi a matsayin Kofur.
Babban Hafsan Sojin Saman ya ce Umar shi ne karamin soja a tarihin rundunar da aka taba gayyato shi tare da iyayensa domin a karrama a Abuja. Daga nan sai ya gode wa iyayaen sojan bisa irin tarbiyyar da suka ba dan nasu har ya samu irin wannan girmamawa da nasara a lokaci kankane cikin rayuwar aikinsa. Sannan ya ba shi takardar gamsuwa da kwazon da ya nuna.
Daga baya Umar ya yi karin haske a kan abin da ya faru inda ya ce suna dawowa daga sintiri ne sai ya hangi kunshin takardar a gefen hanya. Ya ce ya dauki wannan kunshin takarda amma bai yarda abokan aikinsa sun gane me ke cikin takardar ba. “Sai na ga lambar waya a jikin takardar ambulan din. Yayin da muka koma bariki sai na kira wayar sai wani mutum ya amsa na shaida masa cewa mun tsinci wani kunshi, nan da nan sai ya ce ‘eh cikin wata ambula ruwan kasa an rubuta Alhaji Ahmad a jiki.’ Sai ya ce kunshin takardar tasa ce, sai muka shirya da shi cewa za mu hadu da yamma, sai na ce ba damuwa sai ka zo. Ya zo kofar barikin ya ajiye motarsa sannan na karaso wajensa, ya ce min kudin sun kai Yuro 37,000 kudin kasar waje, na mika masa kudin ya kirga ya ce sun cika. Ya yi godiya kwarai da gaske ya ce min me nake so ya saka min da shi, na ce masa ba na bukatar komai albashina ya ishe ni biyan bukatuna. Ya tambaye ni me ya sa ban rike kudin ba na dawo masa da shi. Na ce daidai da sakan daya ban taba tunanin in rike kudinka ba , saboda mahaifina kullum yana fada min cewa kada in yarda in taba kayan wani,” inji Umar.
A shekarun baya da suka wuce ana samun mutane da yawa suna dawo da kudin tsintuwa kamar yadda Umar ya yi ba tare da wani ya yi tunanin rike abin da ya tsinta ba, saboda tarbiyyar wancan lokaci.
Amma a wannan lokaci da muke ciki da za ka tarar da matasa da ake kira da “Yahoo Boys” suna bata lokaci a kan na’urar kwamfuta domin damfarar mutane, tabbas halin kwarai ya zama wani abin mamaki ga wanda ya aikata shi.
Umar ya tabbatar da maganar nan cewa ‘Alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza’ ya yi alheri kuma alheri ya biya shi, ya sanya iyayensa da al’ummar garinsu da abokan aikinsa a cikin halin farin ciki da alfahari.
Babu mamaki yadda Babban Hafsan Sojin Sama ya karrama shi saboda bajintar da ya nuna na halin kirki, saboda a halin da ake ciki zai yi wahala ka amince da gaskiyar jami’an tsaro, lura da irin badakalar da ake samu suna aikatawa ciki har da wadanda suka gudu da makudan kudin wani Janar din soja.