Gwmanati ta ware N263bn don gina tashoshin lantarki a Sakkwato da wasu 4
Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta amince da kashe Naira biliyan N262.75 domin gina tashoshin lantarki a biranen Sakkwato da wasu wurare huɗu
Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta amince da kashe Naira biliyan N262.75 domin gina tashoshin lantarki a biranen Sakkwato da Onitsha da Abeokuta da offa da kuma Ayede.
Za a kashe kuxaxen ne wajen gina sababbin cibiyoyin lantarki masu ƙarfin 330/132 KV da kuma 132/33 KV a wuraren guda biyar.
Ministan Lantarki Adebayo Adelabu, ya shaida wa ’yan jarida bayan taron majalisar a ranar Litinin cewa aikin ya ƙunshi gine-gine da sayen na’urori da kuma hada su, wanda aka ba wa kamfanin Siemens na ƙasar Jamus kwangila.
Adelabu ya ce za a gina sababbin tashoshin ne domin inganta samar da wutar lantarki a Nijeriya a rukuni-rukuni.
- ’Yan Yahoo 159 ’yan kasar waje da ’yan Nijeriya 599 sun shiga hannun EFCC a rana guda
- Jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda 8,034 a 2024
Ya ce a gina tasha mai ƙarfin 330/133 KV kowanne Onitsha. Abeokuta da Ayede kuma 330/132 KV kowannensu, sai Sakkwato 132/33 KV, Offa kuma guda biyu masu ƙarfin 132/33 KV.