Gyara almajiranci ya fi gyaran Najeriya wahala

Wane ne almajiri, kuma mene ne almajiranci?  Mene ne alakar Kur’ani da almajiranci? Wadannan tambayoyi su ne abin da ya kamata mu fara amsawa a kashin kanmu kafin mu kai ga kushe almajirci ko zagin almajirai. Almajiri shi ne wanda yake barin inda yake da yardar iyayensa domin neman ilimin addini wato karatun Kur’ani. Mafi […]

Gyara almajiranci ya fi gyaran Najeriya wahala
Gyara almajiranci ya fi gyaran Najeriya wahala

Wane ne almajiri, kuma mene ne almajiranci?  Mene ne alakar Kur’ani da almajiranci? Wadannan tambayoyi su ne abin da ya kamata mu fara amsawa a kashin kanmu kafin mu kai ga kushe almajirci ko zagin almajirai.

Almajiri shi ne wanda yake barin inda yake da yardar iyayensa domin neman ilimin addini wato karatun Kur’ani. Mafi yawan lokaci iyaye ne suke kai wa malamai ’ya’yansu da kansu domin su yi karatu ko a kusa ko a nesa. Kalmar almajiri ta samo asali ne daga kalmar Almuhajir wadda kalmar Larabci ce da take nufin mai hijira. Ma’ana wadanda yake barin inda yake ko garinsa zuwa wani bangare na jiharsa ko kasarsa domin cimma wani abu da yake so ya samu a rayuwa.

Almajiranci kamar zaman barikin soja ne kowa ka gani a can aiki ne ya kawo shi. Shi ma almajiri in dai ka gan shi a gaban malami to karatu ne ya kai shi. Alakar almajiranci da karatun Kur’ani ita ce mutane masu son addini su ne suke daukar ’ya’yansu su kai duk inda suke ganin za su samu karatun Kur’ani. Almajiranci kamar rayuwar sansani ne daga lokacin da yaro ya samu ilimi ya sauke Kur’ani to zai koma gaban iyayensa domin ci gaba da lamuran rayuwa.

Gwamnatin Tarayya da ’yan majalisar jihohi da sanatoci da ’yan Majalisar Tarayya duk suna da rawar da za su taka a bangaren karatun almajirai. Idan muka duba za mu ga cewa karatun Alkur’ani abu ne wanda ya zamanto wa kowane Musulmi wajibi don zai taimaki mutum tsakaninsa da Ubangijinsa. Ashe kuwa dole a duba wannan lamari mai girman gaske. Harkar almajiranci tana da asali kamar yadda kowane Musulmi ya sani a kasar nan kuma yadda ake kyamar harkar a ganina hakan ba zai taba kawo mana gyara a lamarin ba, don haka ya kamata a yi manhajar da za ta zamanantar ko ta bunkasar da karatun almajirci.

Abin tambaya shi ne wacce gudunmawa aka bayar domin a gyara? Sannan ta wace hanya za a gyara? Ni a binciken da na yi na gano cewa gwamnati ita ce uwa ita ce uba kan gyara wannan lamari. Idan muka kalli tsarin karatun allo a wasu yankuna na Afirka za mu ga ya sha bamban da namu na nan gida Najeriya, wanda hakan kalubale ne a kan gwamnatocinmu. Abu ne mai saukin gaske idan aka ce za a gyara harkar almajiranci a kasar nan idan aka cire son zuciya, amma idan ba haka ba gyaran harkar almajiranci ta fi gyaran Najeriya wahala. Idan ka tambaye ni ta yaya za a gyara harkar? Zan ce maka eh, abu ne mai saukin gaske. Misali muna da Gwamnatin Tarayya muna da gwamnatocin jihohi muna da na kaanana hukumomi. Sannan a karkashin Gwamnatin Tarayya da jihohi da kananan hukumomi akwai masu mukamai daban-daban wadanda suke wakiltar talaka.

Lura da yawan al’ummar da muke da su a Najeriya musamman Arewacin Najeriya wanda a nan ne ake almajiranci, idan kana tunanin ka yi karatun boko ne me zai hana ka taimaka wa wani shi ma ya yi?  Idan kana tunanin talaka ne me zai hana ka zama sanadin yin kudinsa ko fita daga kangin talauci.  Tsanar da ake nuna wa almajirai a kasar nan, ba abu ne wanda za mu zuba ido a ci gaba da yi ba, kamata ya yi mu dauki mataki saboda dukkanmu da su Musulmi ne kuma karatun Kur’ani suke yi. Idan suna kuskure kamata ya yi a san yadda za a yi a dora su a kan hanyar daidai ba a zage su ba.

Yadda za a shawo kan wannan kalubale cikin sauki shi ne gwamnati ta tanadi tsarin kula da makarantun allo kamar yadda take yi ga na karatun boko.  Shi ma almajiri dan kasa ne mai kuri’a kamar kowa. Dole gwamnati ta kalli wadannan abubuwa domin ta hada karfi da karfe wajen samar da gyara a harkar almajiranci a kasar nan. Bayan Gwamnatin Tarayya ta shigar da manhajar karatun addini a tsarin zamani kamar yadda UBE, SUBEB, a karkashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya suke yi,  su ma jihohi da kananan hukumomi su hada karfi da karfe su samar da makamancin haka ga makarantun allo. Sannan su aiwatar da ayyuka kamar haka:

1-Gina makaranta da asibiti da wajen koyon sana’a a kowace karamar hukuma.

2- Shigar da tsarin karatun allo da Islamiyya a cikin tsarin zamani sannan a yi wa malaman albashi.

3-  Sanatoci su kula da bangaren abinci da kayan aikin koyon sana’a

4- ’Yan Majalisar Wakilai su kula da bangaren magunguna.

5- Kananan hukumomi su kuma su kula da tsaro da littatafai

6- Kungiyoyin sa-kai (NGOs) su taimaka da duk abin ake bukata da za su iya.

Mai karatu zai ce wai to yaya za a yi da alarammomi?  To misali idan za ka gina irin wannan makaranta a garin Kumbotso za ka kira taron malamai ka yi musu bita na tsarin da kake so a gwamnatance sannan ka ba su dama duk wanda yake so ya bi tsarin ya yi rajista da gwamnati. Idan ka gina makarantar da tsarin Tsangaya za ka rarraba ta yadda kowane alaramma zai samu bangaren da zai koyar da almarijansa ya dawo gida cikin iyalinsa.

Sannan dole ka samar musu abin hawa da za su je cikin mutunci su dawo cikin mutunci. Hakan shi ne zai sa cikin shekara biyu za ka nemi almajirai masu yawo kan titi ka rasa. Kuma yaro ba zai fito ba sai ya koyi sana’ar hannu, inda zai zama abin kwatance a cikin al’umma.

Ina ganin in dai aka bi wannan tsarin a kowace karamar hukuma a Arewacin Najeriya maganar almajiranci an gama da ita. Amma don ka gina wani wuri a wajen gari ka ce wai malami ya tattara ya koma, ina tabbatar maka hakan ba zai taba yiwuwa ba, domin ba za su iya barin inda suka saba ba. Amma idan aka tsara malami ya je ya ga dalibansa ya ba su darasi ya dawo gida wata ya yi ya samu albashi, to ka taimake shi ka taimaki al’umma kuma kana da kuri’arsu, kai ko tsakaninka da Allah ma muna kyautata maka zaton alheri.

Wadannan abubuwa su ne za su iya kawo gyara da hadin kan al’ummar Arewacin Najeriya kuma hakan zai sa ba za a raina mu ba. Ina fata wannan shawarar za ta samu karbuwa.

Abubakar Muhammad Zain (08035812895)

abubakarmuhammadzain@gmail