Gyara dabi’un matasan Borno ba na cibiyarmu kadai ba ne – Zannah Buguma
Babban Jami’in Cibiyar Horar da Matasa da Sake Dawo Musu da Dabi’u na Kwarai a Jihar Borno, Alhaji Zannah Hassan Buguma ya ce sake inganta rayuwar matasan da rikicin Boko Haram ya rutsa da su ba aikinsu su kadai ba ne, hakki ne da ya rataya a wuyan kowa. Cibiyar tana samun tallafin Bankin Duniya […]
Babban Jami’in Cibiyar Horar da Matasa da Sake Dawo Musu da Dabi’u na Kwarai a Jihar Borno, Alhaji Zannah Hassan Buguma ya ce sake inganta rayuwar matasan da rikicin Boko Haram ya rutsa da su ba aikinsu su kadai ba ne, hakki ne da ya rataya a wuyan kowa. Cibiyar tana samun tallafin Bankin Duniya da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya ne domin inganta halayen matasan yankin Arewa Maso Gabas, kamar yadda jami’in ya shaida wa wakilinmu:
Mene ne dalilin kafa wannan cibiya?
An kafa wannan cibiya ce, domin ta himmatu wajen bai wa matasan yankin Arewa maso Gabas ingantacciyar rayuwa da inganta halayyarsu, wadanda mafi yawancinsu sun shiga cikin wani hali a dalilin rikicin Boko Haram da jihohin shiyyar Arewa maso Gabas ne abin ya fi shafa, musamman jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Bankin Duniya da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno ne ya samar da wannan cibiya, domin ta tallafa wa al’ummar wannan yanki na Arewa maso Gabas ta hanyar koya wa matasa sana’o’i da sake inganta rayuwar wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su. Kuma ayyukan wannan hukuma su ne tabbatar da ganin duk wani dan gudun hijira ya samu tallafi, sannan matasa an koya musu sana’a, a dalilin haka akwai bangarori na tabbatar da yin rajistar dukkan ’yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin ’yan gudun hijira wadanda rikicin ya rutsa da su. A wannan hukuma akan dauki sunayen wadanda lamarin ya shafa a rajistar da muka bude domin sanin adadin wadanda suke sansanin ’yan gudun hijira da wadanda suke a zaune tare da ’yan uwansu a unguwanni, don a tallafa musu da abin da ya kamata. Muna da sassa uku, na daya kudi yake raba wa dukkan wadanda abin ya shafa a sansani ’yan gudun hijirar ko kuma suna gidajen ’yan uwansu, kuma kowane magidanci za a ba shi Naira dubu 200, amma za a raba kudin ne zuwa kashi hudu, akwai wanda kowa da kowa zai karba in dai dan gudun hijira ne. Naira dubu 30, sai kuma na biyu Naira dubu 20 da ake bai wa mutumin da zai koma garinsa bayan an samu zaman lafiya. Wannan yana kasancewa a matsayin alwus ga wadanda suka kudiri aniyar komawa garuruwansu, sannan idan ka je garinka za a ba ka Naira dubu 50, sai abu na karshe a ba ka Naira dubu 100, bayan ka koma gida ka zauna, domin yin jarin fara wata sana’a a inda ka koma.
Zuwa yanzu mun yi rijistar ’yan gudun hijira fiye da dubu 277 a sansanoni daba-daban sama da 43 da cikin unguwanni da kuma garuruwan da aka koma duk mun je an yi wannan rajista.
Na biyu shi ne horar da matasa ’yan gudun hijira ta yin hadin gwiwa da masu sana’o’in hannu don su koya musu duk sana’ar da mutum ya ga ya da ce ya koya.
Ka yi bayanin cewa da har hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya, wane kaso ko tallafi take bayarwa a wannan shirin naku?
Ita Gwamnatin Tarayya a wannan shirin ba ta sanya hannu ba, Bankin Duniya ne da Gwamnatin Jihar Borno da wasu gwamnatocin Arewa maso Gabas da rikicin Boko Haram ya rutsa da su. Kuma su gwamnatocin kashi 10 suke bayarwa cikin kashi 100 sannan kashi 90 na duk tallafin yana zuwa ne da ga Bankin Duniya. To yanzu kuma haka muna kan biyan mutum dubu 47 cikin mutum dubu 277 da muka yi wa rajista.
Wannan tallafin hannu-da-hannu kuke bayarwa ko mutum zai je ya bude asusun ajiya ne a banki ku tura masa?
To wato don a yi gaskiya da adalci a cikin aikin, sai Bankin Duniya ya ce mu za mu rike kudi sannan sai mu nemi duk wani bankin da zai iya yin wannan aikin, kuma muka amince masa shi ke nan sai mu tura musu wannan kudi su kuma sai su tsara yadda za su rika biyan mutanen, To muna dai mun ba su kamar kwantaragi ne suna yi mana aiki, kuma muna biyansu, to amma ka san a Borno in ka debe garuruwan Maiduguri da Biu da Askira Uba, babu bankuna a suran garuruwan da ’yan gudun hijirar suka koma. Da yake akasarin mutanen da ke gudun hijira suna cikin garin Maiduguri, kuma lura da wadansu mutanen da ba su iya zuwa banki ko ba su iya yin hulda da bankuna ba, sai muka bullo da hanya mafi sauki ta zuwa bankin a karshen mako don a ba su kudaden a hannunsu.
Shin kuna bin diddigin mutanen da kuka ba su kudaden a garuruwansu don ganin sun yi amfani da su ta hanyar da ta dace, ba wai su tasa kudin a gaba su cinye ba?
To wannan gaskiya domin mutane idan an ba su irin wannan kudin na taimako, ba bashi ba ne sai ka ga sun tasa kudin a gaba sun cinye kuma su dawo su tsuguna. Sai ka ga kudin bai amfane su ba, don ba sa duba yanayin da suka fada kuma suke cikinsa a yanzu sai su koma yin wani abu daban wani ya yi aure wani ya tasa kudin ya yi ta bushasha, to mu shugabanninsu muke fada, mu ce a ja musu kunnen cewa kada su bar kudin ya tafi a iska ba su yi wata sana’a da shi ba, sai mu ba su shawara ya kamata su rika tunanin jan jari da shi. Bayan haka muna da mutane wadanda aikinsu fadakarwa ga mutanen da suka samu irin wannan tallafi.
A karshe wane kira kake da shi ga matasa don su mayar da hankali wajen neman na kansu?
Kirana su mayar da hankali wajen karatu, tare da neman na kansu komai wahalarsa,yin aikin karfi ka samu na kanka, shi ya fi zama a’ala. Sud aina raina karamar sana’a su rike ta hannu bibbiyu, watakila hakan ne zai rike su a gaba domin duk wanda ka gani da kudi to sai da ya wahala sannan ya same shi. To su ma su yi kokarin ganin su wahala wajen neman na kansu su daina zuwa suna roko ko su zuba wa wani ido ya ba su. Kuma su guji shaye-shaye don ba za su kai su ko’ina ba, wannan shi ne shawara ta ga matasa.