Gyara fatarki da zuma
Zuma ta kasance babban maganin cuttuttuka da dama don haka ya kamata mu kula da ita. A yau mun kawo muku hanyoyin da za a bi a magance cututtukan fata da zuma. Daga ciki akwai; kyasbi da kuraje da tabo da gyaran farce da sauransu. A sha karatu lafiya. •Don magance kurajen fuska : Ana […]
Zuma ta kasance babban maganin cuttuttuka da dama don haka ya kamata mu kula da ita. A yau mun kawo muku hanyoyin da za a bi a magance cututtukan fata da zuma. Daga ciki akwai; kyasbi da kuraje da tabo da gyaran farce da sauransu. A sha karatu lafiya.
•Don magance kurajen fuska : Ana shafa zuma a kan kurajen da suka feso a kullum a kalla safe da yamma. Sannan sai a wanke da ruwan dumi bayan minti goma zuwa goma sha biyar za a ga canji.
•Tabo: Zuma na dauke da sinadaren haskaka fata idan ana shafa shi a kan tabo a kullum a hankali tabon zai zo ya bace.
•Farce: Zuma tana sanya farce kyau. Idan ana da farce mai tauri, za a iya a kwaba zuma da ruwan ‘benegar’ sannan a rika shafawa a farce sai a wanke bayan minti goma.
•kyasbi:A samu zuma mai kyau sai a rika shafawa a kan kyasbin na tsawon minti goma kafin a wanke. Yana da kyau a rika shafawa a kullum na tsawon watanni hudu ba tare da an huta koda na kwana daya ba.
•kurajen aski:Bayan an yi aski ko an aske gemu yana da kyau a shafa zuma a wajen da aka yi aski. A jira na tsawon mintuna goma zuwa sha biyar sannan a wanke. Idan ana hakan zai hana fesowar kuraje.
•Rage gashin jiki: Zuma tana rage gashin jiki. Idan aka hada zuma da ruwan lemon tsami da suga. Sannan sai a tafasa su har sai ruwan ya canza kala. Sannan a sauke a bari ya dan huce. A samu auduga a tsoma a hadin sannan a shafa a fatar jiki inda akwai gashi. Bayan ’yan mintuna kadan, sai a daga audugar. Hakan na cire gashin fatar jiki.
•kunar rana : Zuma na warkar da dabbare-dabbare bakake da ke fitowa a fuska. A shafa zuma a inda ake da matsala sannan a wanke bayan mintuna goma zuwa sha biyar. Yana da kyau a rika gwada irin wannan salon sau biyu a sati domin samun biyan bukata.