Gyara fuskarki da kindirmo

Kindirmo (nono) na gyara fata domin yana dauke da sinadaran da ke kara hasken fata da kuma kare ta daga tabo. A wannan makon mun kawo muku hanyoyin da za ku bi don gyara fuskarku da kindirmo ba tare da kun sha wahala ba. Muna so masu karatu su san cewa za su iya zabar […]

Gyara fuskarki da kindirmo

Kindirmo (nono) na gyara fata domin yana dauke da sinadaran da ke kara hasken fata da kuma kare ta daga tabo.
A wannan makon mun kawo muku hanyoyin da za ku bi don gyara fuskarku da kindirmo ba tare da kun sha wahala ba. Muna so masu karatu su san cewa za su iya zabar daya daga cikin hanyoyin da muka kawo muku, kada ku hada duka wadannan hanyoyin domin yin hakan zai janyo illa.
·        Zuma da lemon tsami da kindirmo;  Ku hada zuma da lemon tsami da kindirmo a cikin kwano ko roba sai ku kwaba su sosai, sannan ku shafa a fuska har zuwa wuyanku, sai ku jira na tsawon minti 15 kafin ku wanke.
·        Kindirmo da tumatir: Ku yayyanka tumatir, sannan ku yaryada siga kadan kafin ku zuba kindirmon a kai. Sai ku dauki tumatir sannan ku shafa a fuska da wuya da hammata da kuma hannu, sannan ku jira na tsawon minti 10 kafin ku wanke.
·        Lemon zaki da kindirmo; Ku wanke fuskarku, sannan ku watsa wa fuskar ruwa, daga nan ku matse ruwan lemon a cikin kindirmo, sannan a gauraya, sai ku  shafa a fuska da wuya, sannan ku bari na tsawon minti 20 kafin ku wanke da ruwan dumi.
Idan kuna son cin nasara, za ku iya amfani da wannan hadin na tsawon wata daya, inda za ku rika shafawa sau daya a rana.