Gyara jikinki da man kwakwa
Assalamu alaikum, Uwargida tare da fata ana lafiya. Ya kamata mace ta kasance cikin gyaran jikinta musamman ga matan aure. Wata matar daga aure shi kenan sai kamanninta ya canza kamar ba ita aka auru ba. Ina gargadi gare ku da ku kasance masu gyara jikinku yadda ko ‘yan mata sai sun yi da […]
Assalamu alaikum, Uwargida tare da fata ana lafiya. Ya kamata mace ta kasance cikin gyaran jikinta musamman ga matan aure. Wata matar daga aure shi kenan sai kamanninta ya canza kamar ba ita aka auru ba. Ina gargadi gare ku da ku kasance masu gyara jikinku yadda ko ‘yan mata sai sun yi da gaske kafin su tadda ku a fannin kwalliya. A yau na kawo muku hanyoyi da dama wajen gyara jiki da man kwakwa. |
• Kurajen fuska; yana da kyau a kasance ana amfani da man kwakwa wajen girki domin rage kurajen fuska. Sannan za a iya shafawa da dan auduga kadan a kan kurajen da ya feso a fuska a kullum na tsawon mako biyu kafin a shiga wanka za a ga canji.
• Sanyi; domin magance ciwon sanyi da ke damun mata da dama, za a iya wanke inda ciwon yake a busar sannan a sami man kwakwa a rika shafawa a wajen amma sai anyi hakuri. A kullum za a rika shafawa har sai sanyin ya tafi. Ana so a rika shafawa kamar sau biyu zuwa uku a rana.
• Ciwon hakori; ciwon hakori na sanya warin baki don haka dole ne a nemi hanyar magance ta ta hanyar amfani da man kwakwa. A sami auduga a tsoma a cikin man kwa-kwa sannan a rika shafawa a kan da gefen hakorin da ke yin ciwo na tsawon minti biyar. Za a iya rika amfani da shi a kan magogin wanke hakori a kullum za a ji sauki.
• Kurajen yara; za a iya rika shafa man kwakwa a jikin yara kanana domin gyara musu fatar jiki kuma za a iya shafa masu kafin a sanya musu wando a gabansu bayan wanka. Yana kare kananan kuraje daga feso musu.
• Rage kiba; domin rage kiban jiki, yana da kyau a riga amfani da man kwakwa wajen yin kowane girki. Man na rage kiba kuma ya kara kuzari a jiki.
• Domin hasken hakori; murmushi mai kyau na kara wa mace kyau musamman idan hakoran sun kasance farare tas. Don haka yana da kyau a rika goge hakori da auduga da man kwakwa a kullum domin samun sakamako mai kyau.