Gyara kayanka (1)

Idan akwai wani abu da ya kamata duk wani Sarki da zai zo bayan Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya yi koyi da shi bai wuce irin yadda ya iya zama lafiya da gwamnonin da ya yi zamani da su. ba Ba za mu kai ta da nisa ba, mu tsaya a iya dawowar mulkin […]

Gyara kayanka (1)
Gyara kayanka (1)

Idan akwai wani abu da ya kamata duk wani Sarki da zai zo bayan Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya yi koyi da shi bai wuce irin yadda ya iya zama lafiya da gwamnonin da ya yi zamani da su. ba Ba za mu kai ta da nisa ba, mu tsaya a iya dawowar mulkin dimokuradiyya a Jamhuriya ta hudu.

Gwamnan farko da Kano ta yi shi ne Sanata Rabi’u Kwankwaso. Hakika Sarki Ado ya zauna lafiya da gwamna Kwankwaso a zuwansa na farko. Ya ba shi cikakken hadin kai da goyon baya akan duk manufofinsa a fannoni daban-daban kamar ilmin primary, samar da lantarki a kauyuka, da sauransu. Wannan ya taimakawa gwamna Kwankwaso wajen samun gagarumar nasara a wadannan bangarori. Gwamna Kwankwaso ya fara samun matsala da mutanen Kano sakamakon sanyin jiki da ya nuna a al’amarin aiki da Shari’ar musulunci wacce guguwarta ta ke kadawa da karfi a wancan lokaci. Duk da cewa ya yarda ya kaddamar daga karshe, wannan bai hana Kanawa su kifar da gwamnatinsa ba. Abin mamaki shi ne har lokacin da alaka tai tsami tsakanin gwamna Kwankwaso da Kanawa, Mai Martaba Sarki Ado bai taba kwarewa gwamna baya ba a bainar jama’a. Ya ci gaba da ba shi hadin kai har hakan ta sa Gwamna ya ga dacewar ya saka masa ta hanyar radawa wannan babban gini na Kofar Nassarawa sunansa ba dadewa bayan yi masa kwaskwarima. Saboda yadda alaka ta ke da kyau tsakaninsu, Gwamna har daukar Sarki ya yi su ka je Abuja taya tsohon Shugaban Kasa Obasanjo murnar cin zabe karo na biyu, abinda ya kara fusatar da mutanen Kano sakamakon rashin kaunarsu da Kwankwaso da Obasanjon a wancan lokaci.

Wannan ya na nuna Sarki Ado bai damu da ra’ayin jama’ar Kano ba ne? Ko kadan! Hakan ya na nuna ya san me ya kamata ya yi a matsayinsa na Sarkin gargajiya wanda ba shi da iko a hannunsa.

Bayan Kwankwaso sai Malam Ibrahim Shekarau. Irin alakar da Sarki yai da Kwankwaso ya jawo mishi bakn jini a gurin magoya bayan sabuwar gwamnati. Idan ba mu manta ba har jifan Mai Martaba aka yi a filin rantsuwa kamar yadda aka dinga yi wa Kwankwaso a karshen mulkinsa. Haka ne ya sa bayan rantsuwa gwamna bai zame ko ina ba sai gidan Sarki don ba shi hakuri da nuna rashin goyon bayansa ga abinda ya faru. Lafawar wannan kura ke da wuya sai aka bude sabon babi na kyakkyawar alaka da mutunta juna tsakanin gwamna da Sarki irin wadanda ba a taba ganin irinsu ba a tarihin Kano. Sarki ya bawa gwamna cikakken hadin kai a duk manufofinsa na gina dan Adam da taimakon addini. Da kansa ya dinga zuwa garuruwa kaddamar da shirin gwamnati na gyaran tarbiyya mai taken A Daidaita Sahu. A shekaru takwas din da su kai ba a taba samun wani rashin fahimta tsakanin Sarki da gwamna ba har sai da ta kai Sarki ya nada gwamna mukamin Sardauna saboda dadin zama da mutuntawa da ke tsakaninsu. Ta kai jallin da sai da tsohon gwamna Kwankwaso ya taba turowa a gargadi Sarki ya nisanta kansa da gwamnatin Shekarau. Ina tuna jawabin Sanata  Mas’ud Doguwa a gaban Sarki wajen isar da wannan sako na Kwankwaso.

Irin shakuwar da ke tsakanin Sarki Ado da gwamna Shekarau ce ta sa Gwamna Kwankwaso ya dawo da haushin Sarki a zuwansa na biyu. Tun ana kamfe ake kirarin “sabon gwamna sabon sarki” wanda ya ke nuna irin niyyar da su ke da ita na cire Sarki sakamakon yadda su ke ganin kusancinsa da gwamnatin Shekarau. Sarki ya lura da wannan amma bai tanka musu ba kuma da su ka dawo ya cigaba da ba su hadin kai sosai kamar yadda ya ke yi koda yaushe. A lokuta da dama ya yabawa yunkurin gwamnati na kakkafa makarantu don samar da sana’a ga matasa da kuma kunna fitilu don haskaka Kano da daddare. Tsananin biyayya da taka tsantsan ya sa dole aka kasa cire shi duk da cewa ya fuskanci tsangwama iri-iri kamar hana shi hawa a wata sallah da warware nadin waziri da ya yi. Sarki Ado ya yi hakuri, ya yi juriya har Allah ya karbi ransa ya na cewa ba shi da matsala da kowa a Jihar Kano.

A takaice abinda wannan ya ke nunawa dole ne Sarki ya bi gwamna idan ya na so a zauna lafiya. Idan ya na da shawara ga gwamnati dole ne ya bi hanya mafi dacewa ya isar da ita. Ba don bai san gaskiya ba ko ba ya son gaskiya ba, ban taba jin Marigayi Sarki Ado ya na sukar wata gwamnati ko wani gwamna a bainar jama’a ba. Haka nan ya yi kokari matuka wajen janye jikinsa daga harkokin siyasa.

Wannan duk akan idonmu ya faru ba wani ne ya gaya mana ba, ba kuma a littafi mu ka karanta ba. Da wayonmu mu ka ga wannan saboda haka ba za mu yarda wasu ‘yan rudu su yi wasa da hankalinmu ba. A kashi na biyu inshaAllah za mu nazarci yadda Mai Martaba Sarki Sanusi II ya rayu da gwamnonin da yayi aiki da su izuwa yanzu.

Ibrahim Sirajj Adhama

[email protected]