Gyara kayanka (2)

Allah cikin ikonSa Ya gadar wa Sarki Sanusi II Gidan Dabo. Mun yi murna kwarai da zuwansa kasancewarsa mutum mai ilmi bangare biyu. Mun yi fatan zai yi amfani da ilminsa da kwarewarsa da mutane da yake da su a fadin duniya wajen jawowa Kano ci gaba mai yawa. Abin da ya kara min farin […]

Gyara kayanka (2)
Gyara kayanka (2)

Allah cikin ikonSa Ya gadar wa Sarki Sanusi II Gidan Dabo. Mun yi murna kwarai da zuwansa kasancewarsa mutum mai ilmi bangare biyu. Mun yi fatan zai yi amfani da ilminsa da kwarewarsa da mutane da yake da su a fadin duniya wajen jawowa Kano ci gaba mai yawa. Abin da ya kara min farin ciki shi ne yadda na fahimci wanda na ke goyon baya a gidan Marigayi Ado Bayero ba shi zabi ya fada kansa ba.

Da farko an so a kawo mana rudani game da akidarsa amma tun kan a je ko ina wasu daga cikin malamanmu wadanda muka yarda da su su ka gamsar da mu cewa ba dan shi’a ba ne kamar yadda wasu su ka fara yadawa.

Mun dafawa sabon Sarki da addu’a da fatan alkhairi a lokacin da mutane da yawa su ka kasa sallamawa. Mun tafka muhawara mai zafi da masu adawa da hawansa kuma mun yi nasara wajen gamsar da yawa daga cikinsu.

Muna kyakkyawan fata ga Sarki Sanusi kuma kaunarmu da shi ta na da yawa kwarai.

In ban da Allah wanda ya kaddara zuwansa, ba wanda Sarki Sanusi ya kamata ya gode wa kuma ya yi masa biyayya kamar tsohon Gwamna Kwankwaso wanda a zahiri shi ne Allah ya tabbatar da lamarin ta karkashinsa. Alhamdulillah, an fara lafiya cikin kauna da girmama juna tsakanin gwamna da sabon sarki. Amma abinka da “Dan koyo” kafin a je ko ina sai ga shi an fara samun rashin jituwa. Sarki ya kasance ya na tara talakawa mabukata ya na musu rabon abinci a kofar gidansa. Ba mu san dalilin gwamna Kwankwaso ba kawai sai mu ka ji ya ba da umarnin a dai na wannan rabon tallafi. A karo na farko a rayuwata na ji Sarki ya shiga radio ya na martani ga gwamna ya na cewa da kudinsa ya ke yi ba da na wani ba. Wannan abin mamaki ne kwarai ga wanda ya san alakar Sarki Ado da gwamnoninsa kamar yadda ya gabata a kashi na daya. Abin ya yi kamari har ta kai jallin da gwamna ya gargadi Sarki ya ba shi abinda ake kira takardar tuhuma ‘kuery’. Wannan tun zamanin Kwankwaso ya faru wanda shi ya nada shi. Yara sun manta wannan sai su dinga nuna kamar da Ganduje ne Sarki ya fara samun matsala.

Bayan zuwan gwamna Ganduje, sarki Sanusi sai ya fara nuna halayyar da ta sabawa matsayinsa na Sarki inda ya fara fitowa fili ya na kushe wasu daga cikin manufofin gwamnatinsa. Ma fi muni shi ne jawabin da ya yi a Kaduna inda ya dira akan gwamnati yayi kaca-kaca da shirinta na samar da sabon tsarin sufuri a jihar Kano. Wannan ya girgiza gwamna kwarai da gaske kasancewar irin girman da ya ke ba shi. Idan zai gaida sarki a taro har kirari ya ke yi masa da Fulatanci. Wannan shi ne ya haddasa rigima ta farko mafi girma tsakanin gwamnatin Ganduje da Sarki har ta kai ga yunkuri na farko na cire shi.

Allah ya taimaka an ga karshen wannan rigima sakamakon shiga tsakani da wasu shugabanni su ka yi amma duk da haka alaka ba tai kyau sosai yadda ya kamata a tsakakinsu ba. Duk da cewa an yi alkawari Sarki zai ja girmansa kuma an karbi uzurinsa na cewa shi sabon shiga ne amma an ci gaba da samun karya alkawari nan da can. Ana haka kuma sai wannan bakar siyasar ta 2019 ta zo inda gwamnati take zargin cewa Sarki ya mara wa ‘yan adawarta baya don a kifar da ita. Ban san gaskiyar wannan zargin ba saboda haka ba zan iya cewa komai a kai ba. Abin da na sani kawai shi ne hakika Mai Martaba Sarki Sanusi II ya yi kasa a gwiwa wajen gudanar da al’amuransa musamman abin da ya shafi alakarsa da gwamnati kamar yadda ya kamata a matsayinsa na Sarkin gargajiya kuma uba ga kowa.

SHAWARA

Duk da wannan matsaloli ina ganin bai kamata mu samu kanmu a wannan rudun da mu ke ciki a yau ba. Bai kamata gwamna ya ce sai ya dau fansa ba musamman ta hanyar keta masaurautar Kano ba. Kamata ya yi ya hakura ya nemi hanyoyin da zai ja hankalin Sarki akan abinda ya ke ganin ya yi masa na kuskure. Ba wani amfani na sosai da keta Kano zai kawo sai ma dai ya kara raba kawunan mutane idan ba a wayar musu da kai yadda ya kamata ba. Muna ganin abinda ya ke faruwa a JiharJigawa wacce mu ka hada abubuwa iri daya da ita.

An yi rashin sa’a a Kano wasu mutane da su ke kiran kansu ‘yan jarida duk lokacin da aka samu wata baraka maimakon su tsaya su fito da gaskiyar lamari a ba wa mai laifi laifinsa sai su koma bangare daya su na abubuwa na son zuciya. Wadannan ba masoyan Sarki na gaskiya ba ne ni a fahimtata. Abinda su ke yi ba ya taimakawa wajen fahimtar yadda matsalar ta ke don a warware ta. Ko a lokacin Kwankwaso da aka fara samun matsala haka su ka shiga su ka tsagalgale su na nuna Sarki ne da gaskiya gwamna ba shi da ikon ya hana shi abinda ya ke tinda taimako ne. Sun manta biyayyar gwamna dole ce a kansa. Haka ma wasu kwamared-kwamared na karya su ke taimakawa wajen dagula al’amura a jihar Kano. Allah yai mana maganinsu. Ba ma goyon bayan keta Kano musamman saboda fansa akan Sarki Sanusi amma kuma ba ma goyon bayan  Sarki ya dinga zubar da girmansa ta hanyar maganganu a guraren da ba su dace ba ko goyon bayan wani bangare na siyasa domin wannan ya sabawa matsayinsa na uba. Allah ya taimaki Jihar Kano. Allah ya zaunar da mu lafiya kuma ya albarkaci rayuwarmu.

Daga karshe na yi wannan rubutu ne don bayar da gudunmawa wajen neman zaman lafiya a Kano ba don goyon bayan wani bangare ba. Allah ya karbi ibadunmu a wannan wata mai alfarma na Ramadan!

Ibrahim Sirajj Adhama

[email protected] 0803 592 3734