‘Gyara sufurin jiragen kasa zai rage talauci’
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gina karin layin dogo a shiyoyyin kasar nan shida tare da gyaran tsofaffin layin dogon da maye gurbinsu da na zamani. Aminiya ta zanta da Shugaban kungiyar M a’aikatan Jiragen kasa ta Najeriya kuma Turakin Paiko, Kwamared Sa’id Garba inda ya yi tsokaci […]
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gina karin layin dogo a shiyoyyin kasar nan shida tare da gyaran tsofaffin layin dogon da maye gurbinsu da na zamani. Aminiya ta zanta da Shugaban kungiyar M a’aikatan Jiragen kasa ta Najeriya kuma Turakin Paiko, Kwamared Sa’id Garba inda ya yi tsokaci kan alfanun yunkurin na Shugaba Buhari. Kuma ya bayyana abin da ya nakasa sufurin jiragen kasa a Najeriya da hanyoyin da ya kamata gwamnati ta bi wajen farfado da shi:
A yanzu da Shugaban kasa Buhari ke kokarin inganta sufurin jiragen kasa, wane hali wannan sashi ke ciki a yanzu?
A gaskiya wannan yunkuri na Shugaban kasa Buhari abu ne mai muhimmanci da muke maraba da shi, domin kowa ya san Shugaban mutum ne mai fada-da- cikawa, don haka mun yi murna kwarai saboda muna da yakinin wannan kwangila da Shugaba kasa ya bayar dama mu a bangarenmu na ma’aikata abin da muke nema ke nan. Domin in ka dubi halin da sufurin jiragen kasa ke ciki kafin zuwan wannan gwamnati abin ya yi muni domin babu injuna, babu taragogin jiragen duk abin da ake bukata a wannan fanni na sufuri babu.
To ka yi maganar babu isassun kayan aiki duk da a baya da wannan hanya ta sufuri kasar nan ta dogara yaya aka yi?
Idan ka lura tun daga lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo na farar hula babu irin alkawuran da ba a yi ba inganta sufurin jiragen kasa amma babu wani abin a zo a gani da aka yi. Layin dogon da muke amfani da shi ba shi ne wanda duniya ta amince da shi a yanzu ba. Namu ya zama tsohon yayi sai a wannan gwamnati ne aka fara sauya layin dogo ana mai da shi na zamani. A yanzu haka in ka tashi tun daga Oyinbo a Legas har zuwa Abeokuta an fara fadada hanyar ana rushe-rushe don zamanantar da layin ya zama daidai da wadanda ake amfani da su a kasashen da suka ci gaba. Tun lokacin Obasanjo aka ba da kwangilar sauya layin dogo amma shiru, babu amo babu labari amma da wannan gwamnati ta kaddamar da aikin an fara aikin gadan-gadan kowa na gani.
Dama layin dogon da muke amfani da shi a kasar nan ba wanda aka yarda a yi amfani da shi ba ne?
Eh ka san muna amfani da karamin geji ne na layin dogo, wannan karamin da muke amfani da shi ya zama tsohon yayi domin yana da illa sosai shi ke sanya jirgin kasa yawan faduwa domin fadin karfen da muke amfani da shi inci 3 ne da santimita 5 kuma ana so a maye gurbinsa da na zamani mai inci 4 da santimita 5. Na zamanin jirgin ba ya yawan faduwa sosai. Kuma in aka lura kasashen duniya sun yi gaba a wannan sha’ani, sun wuce maganar layin dogo na zamani, suna batun jiragen kasa na karkashin kasa ne.
Akwai kasashen Afirka da suka ci gaba a wannan fanni na sufurin jiragen kasa me kake ganin ya haifar da sukurkucewarsa a Najeriya?
Matsalar cin hanci da rashawa ita ta gurgunta sha’anin sufuri a kasar nan domin gwamnatocin baya sun yi ta fitar da makudan kudi domin yin gyara amma sai a yi rub-da-ciki da kudaden, an karkatar da su domin cin hanci ya zamo ruwan dare a wannan kasa tamu daga kasa har sama.
Wane irin sauyi kake gani za a samu a kasar nan idan mahukunta suka gyara sufurin jiragen kasa?
Gyara harkar sugurin jiragen kasa abu ne da zai kawo babban sauyi a kasa baki daya, sai dai lamari ne mai kamar wuya domin manyan kasar nan ne suka mallaki manyan motocin da suke safarar kayayyaki irin su man fetur da kayayyaki. Irin wadannan mutane ba za su yarda sufurin jiragen kasa ya inganta ba. Zan iya tunawa wani lokaci da kamfanin mai na Oando ya fara safarar man fetur ta jiragen kasa a wancan lokaci an samu sauki faduwar manyan motocin dakon man fetur amma daga baya aka yi wa lamarin zagon kasa. Idan aka lura hanyoyin kasar nan, manyan motocin daukar kaya ne musabbabin lalacewarsu, kuma duk gyaran da za a yi ga hanyoyin nan muddin manyan motoci za su ci gaba da daukar kayayyaki masu nauyi za a ci gaba da zama a gidan jiya ne. Kayan da ya kamata mota 3 ko 4 su dauka sai a ce mota daya ce za ta yi dakonsu.