Gyara tsarin makarantun allo: Sai kowa ya kama
Tsarin karatun makarantun allo da akan aika yara kanana ’yan shekara biyar zuwa shida garuruwa daban-daban a wasu jihohin Arewa da sunan almajiranci, wato neman Alkur’ani, tsohon tsari ne da Turawan mulkin mallaka suka tarar da mutanen Arewa sun gada iyaye da kakanni. Yayin da su kuma Turawa suka zo da nasu tsarin karatun da […]
Tsarin karatun makarantun allo da akan aika yara kanana ’yan shekara biyar zuwa shida garuruwa daban-daban a wasu jihohin Arewa da sunan almajiranci, wato neman Alkur’ani, tsohon tsari ne da Turawan mulkin mallaka suka tarar da mutanen Arewa sun gada iyaye da kakanni. Yayin da su kuma Turawa suka zo da nasu tsarin karatun da ake kira da karatun boko. Tsohon malamin makaranta kuma tsohon Minista a Jamhuriyya ta Biyu, marigayi Alhaji Bilyaminu Usman (Allah Ya gafarta masa), ya taba fada mini ma’anar wadancan kalmomi. Ya shaida mini cewa karatun boko ana nufin karatun littafi, kasancewar sunan littafi da Ingilishi shi ne book, shi kuma karatun Bature daga littafi ake yin sa, don haka Hausawa suka sa masa suna karatun boko.
Turawa ba su sanya mana baki a kan tsare-tsaren zamantakewarmu da addininmu na Musulunci ba, bare kuma al’adunmu, duk kuwa da sun dukufa a kan yada karatun boko da addinin Kirista.
A Arewa sun yi mulki ne ta bayan fage, kasancewar sun tarar da sarakunanmu suna da nasu tsarin gudanar da mulkin da ya yi wa Turawan daidai. Alhali a Kudu sun rika gudanar da mulki kai-tsaye ne, kasancewar sun tarar da su ba su da wani takamaiman tsarin tafiyar da mulki. Turawa ba su fuskanci wasu matsalolin a je a karar ba a Kudancin kasar nan wajen yada manufofinsu, kamar yadda suka samu a Arewa daga Hausawa da Fulani, kasancewar mutanen Arewar suna gani da karfin tsiya Turawan suka ci su da yaki kuma suna neman su rusa addinin Musulunci ne baki daya.
Hakan ya sa a Arewa ta kai fagen da malaman addini da suka yi zamani da Turawan, suka rika ba da fatawar cewa wanda ya kai dansa makarantar allo ko ya aurar da ’yarsa sadaka, to, ya yi sadaka mai gudana, ta yadda wadanccan ayyuka da ya yi za su cece shi a Ranar Alkiyama. An ce malaman sun samu wannan fahimta ce daga Hadisin da yake maganar yin sadaka mai gudana da ko bayan mutum ya mutu za a rika rubuta masa lada a kan ayyukan alherin da ya shuka. Cikinsu kuwa har da haihuwar dan da ya samu shiriya, ya kuma rika yi wa iyayensa addu’ar nema musu gafara bayan mutuwarsu.
Haka aka taho, al’ummar Hausawa da Fulani suka ci gaba da nuna kyama da kiyayya a kan karatun boko, tun ana ba iyaye kudi in an sa ’ya’yansu a makarantar boko, har ta kai ana yi wa iyaye ta karfin mulki ana sa ’ya’yansu karatun bokon.
Dattijo kuma tsohon Minista a Jamhuriyya ta daya, marigayi Alhaji Shettima Ali Monguno, (Allah Ya gafarta masa) wani lokaci a 1983, ya taba fada mini cewa lokacin da aka sa shi makarantar boko sai da aka rika ba mahaifiyarsa taro duk wata don a faranta mata rai a kan an dauki danta an kai makarantar boko ko an kai wajen Turawa.
Haka aka yi ta karatun bokon a daddafe, har Allah Ya kawo mu a yau da kusan kowa yake ganin amfanin karatun bokon ko a karan kansa, ko a cikin ’ya’yansa ko a gidan makwabcinsa ko a kauyensu.
Bokon da a yau, ya zama a yi ba don a samu aiki ba, sai don a cikasa mutuncin kai da na addini da ma na al’umma. Kasancewar abokan zamanmu na Kudu har gobe suna kallonmu ’ya’yan masu kiwon shanu kuma muna mallakarsu.
Duk irin wannan tafiya da aka yi a kasar nan koma daga samun ’yancin kan kasar nan daga Turawan mulkin mallaka da ake da kusan shekara 59, har gobe akwai masu kyamar tura ’ya’yansu a makarantun boko, ba wai don ba su da kudin da za su rika daukar dawainiyar karatun bokon ba, a’a sai don kawai ba su yarda da tsarin karatun bokon ba. Amma kuma alhamdulillahi, wadansu daga cikin wadanda tsarin karatun allon ya haifa, suka kuma taso cikin tsarin barace-baracen da ake ganin yana kara kawo kaskanci a cikin rayuwar almajiran da ma al’ummar Hausawa da Fulani da yawa sun daina tura ’ya’yansu zuwa almajiranci da sunan karantun allo. Wadansu kuma da suke cikin tsarin koyar da karatun allon, sun zamanantar da shi, ma’ana almajiransu ba sa bara balle kuma zama cikin datti, inda malaman kan sa wa iyaye kudaden daukar dawainiyar karatun ’ya’yansu.
Wani babban abin takaici shi ne tun daga lokacin da aka fara samun rikicin Maitatsine a Kano a 1980, da irin sa da aka samu a Maiduguri da Gombe, duk a shekarun 1980. Da rikicin Boko Haram da yau ake fama da shi a jihohin Arewa maso Gabas yau shekara goma, kullum mahukunta suka motsa da ma sauran ’yan kasa dora alhakin irin wadannan rikice-rikice suke a kan almajiran makarantun allo.
Ko a makon jiya an ji Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), a wata ganawa da manema labarai bayan kaddamar da sabuwar Majalisar Tattalin Arzikin Kasa, a Abuja, yana fada wa duniya cewa akasarin rrikice-rikicen Boko Haram da ta’addanci irin na garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sace-sacen shanu da hare-haren ba gaira ba dalili da ake ta fama da su a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna, Gwamnatin Tarayya tana duba yiwuwar haramta tsarin almajiranci na makarantun allo, don ta shawo kan matsalolin tsaro da kasar nan take fuskanta.
Amma a karin haske a kan wancan furuci na Manjo Janar Monguno an ruwaito Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu, yana cewa duk da yake haramta almajirancin shi ne mafi a’ala, amma ba yanzu ba.
Malam Garba Shehu ya kara da cewa ko kusa ba mu son mu jefa tsoro a cikin zukatan iyaye a kan daga wancan furuci za a shiga kama su, illa dai abin da Shugaban Kasa ya fadi cewa bai wa kowane yaro ilimin firamare da karamar sakandare kyauta, shi kadai ne hanyar da za a iya magance matsalar almajiran.
Tabbas, masu iya magana kan ce kisan baki sai taro, maganar magance matsalar almajiran makarantun allo, matsala ce da ta shafi iyayen yara da malaman makarantun allon da gwamnatoci da sauran al’ummar Annabi. Sai kuma kowa ya taka tasa rawar yadda ya kamata za a kai ga nasara.
Iyaye ya kamata su san cewa lokaci ya wuce da za su rika tura yaransu irin wannan tsarin karatu ba tare da ba da tasu gudunmawar ba, ta daukar dawainiyar ’ya’yansu kan abin da ya shafi ci da sha da tufatar da su. Haka su ma malamai su sani cewa ko me za a ba su a kan su karantar da yara Alkur’ani ba a biya su ladarsu ba, don haka su daina cewa don Allah suke koyar da almajiran, su rika sa wa iyayen yara kudi ko abinci har ma da sabulun wanka da wanki don tsabtar ’ya’yansu, kai har ma da na kudaden inda yaran za su rika kwana.
Ita kuma gwamnati tun daga kan ta karamar hukuma zuwa ta jiha zuwa ta tarayya lallai su san irin yadda za su rika shigowa suna taimaka wa almajiran makarntun allo da malamansu, kamar dai yadda suke daukar dawainiyar karatun boko gwargwadon zarafi. Sauran mutane kamar yadda suke taimakawa wajen tafiyar da manya da kananan makarantun boko, haka ya kamata su rika tallafa wa marantun allon. An dai ce kisan baki sai taro, don haka yanzu ne ya kamata kowa ya sa hannu a cikin wannan muhimmin al’amari na duniya da Lahira, mu daina neman mace ci nesa.