Gyaran Dokar Zabe: Ba a Tuntube mu ba —CJ
Alkalin Alkalan Kotun Tarayya John Tsoho ya ce majalisar dokoki ba ta tuntube su ba kafin sabunta dokar zabe ta 2022.
Alkalin Alkalan Kotun Tarayya John Tsoho ya ce majalisar dokoki ba ta tuntube su ba kafin sabunta dokar zabe ta 2022.
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a jawabinsa na wani zama na musamman da kotun ta gudanar a Abuja.
- Zan kawo karshen ’yan bindiga cikin kankanin lokaci —Tinubu
- An Cafke ’Yan IPOB Da Suka Kai Hari Ofishin INEC A Imo
Ya ce karkashin sashi na 29 (5) da na 84(14) na dokar, Kotun Tarayyar ce kadai ke da ikon saurare da kuma yanke hukunci game da kararrakin gabanin zabe.
“Karkashin sashi na 285(10) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kuma, dole ne a kammala yanke hukunci kan kararrakin gabanin zabe kwanaki 180 bayan shigar da kara.
“Wannan kuma bai hada da kararraki masu dimbin yawa da alkalai ke fama da su a kotunan Najeriya ba.
“Don haka ya zama dole su bayyana cewa sabunta dokar zabe ta 2022 da aka yi, ba a tuntubi kotunan ba.
“Har ila yau, babu wani tsari da aka tanada kan wannan nauyi da aka karawa kotunan,” in ji shi.