Gyaran gangar Abzinawa kan kamusun karin maganar Hausa
A gaskiya raddi ko sukar-lamiri ko kuma nakidancin da dan’uwa Sharafaddeen Sidi Umar ya yi wa littafin kAMUSUN KARIN MAGANAR HAUSA Wallafar Farfesa Ibrahim Malumfashi da Nahuce Marafa Ibrahim abin a yi maraba da shi ne kwarai da gaske a da’irar nazarin harshe. A da’ira ta nazarin harshe, tun da an sami al’ummomin da suka […]
A gaskiya raddi ko sukar-lamiri ko kuma nakidancin da dan’uwa Sharafaddeen Sidi Umar ya yi wa littafin kAMUSUN KARIN MAGANAR HAUSA Wallafar Farfesa Ibrahim Malumfashi da Nahuce Marafa Ibrahim abin a yi maraba da shi ne kwarai da gaske a da’irar nazarin harshe.
A da’ira ta nazarin harshe, tun da an sami al’ummomin da suka riga al’ummar Hausawa taka rawa wajen tabbatar da ka’idodi babu yadda za a yi a kawar da kai daga gaskiyar lamari.
Al’ummomin da suka riga al’ummar Hausawa taka rawa a fagen Ilimi a gurguje su ne Girkawa da Rumawa da Sinawa da Indyawa da Farisawa da kuma Larabawa sai kuma a karshen karni na faduwar daular Usmaniyya ta Shehu danfodio (1754 – 1817) Turawan Ingilishi suka zo mana da rubutun Boko (Roman Manuscripts).
Turawan sun sami nasarar kawar da rubutun Ajami (Arabic Manuscripts) sannu a hankali har sai da rubutu da haruffan Rumawa ya maye gurbin Ajami ana gani ana ji babu yadda aka iya.
A gurguje dai ko shakka babu harshen Hausa ya sami tagomashin zama harshen da ake nazarin sa a dukkan matakan karatu a Nijeriya da sauran kasashen Duniya ciki har da Turai da Amirka.
Idan aka nazarci sukar lamurin (Criticism) da dan’ uwa Sharafaddeen ya yi wa littafin kAMUSUN KARIN MAGANAR HAUSA a tsanake za a ga cewa, habaicin nan da Hausawa ke yi, ya yi aikinsa sosai (kunkuru ya so dambe, sai dai dantse ya gaza) domin kuwa kusan dukkan sukar da ya yi wa littafin shi ma ya gamu da shi, domin kuwa ya auku a cikin rubutunsa.
Idan aka nazarci sukar-lamiri (Criticism) da Sidi Umar ya yi wa littafin kAMUSUN za a ga cewa, bai yi la’akari da bangaren da ya yi suka ba ganin cewa bai fayyace daki-daki mene ne takamaimai yake son ya nusar ba ganin cewa, fiye da kashi 99 cikin 100 na wadanda suke karanta jarida ko sauraron rediyo ba su da ilimi kan nazarin harshen Hausa a kowane mataki na karatu.
Abin nufi a nan shi ne idan aka kalli Hausa a matsayin harshen Hausa za a iya shiga garari wajen fahimtar inda littafin da mai sukar sa suka sanya gabansu. Shin suna koyar da ka’idar rubutun Hausa (Morphology) ne ko salo (Style) ko ta’arifi (Définition) ko gyaran fuska (Terminology) ko kuma ginuwar magana (Syntad)? ka ga an sanya masu karatu cikin taraddadi.
Abin da mai sukar-lamirin bai yi la’akari da shi ba shi ne ko-in-kulan da masu buga rubutun Hausa (Compositors) ke yi wa Hausa idan aka ba su aikin bugawa (Type settings). Sai kuma irin tsarin da aka dora na’urar Kwamfuta a kai (Programming) duk suna da tasiri wajen bata tsarin rubutun Hausa, misali, idan aka rubuta ‘ita ce’ sai kwamfuta ta mayar ‘it ace’ sai kalmar ‘damar’ sai kwamfuta ta mayar ‘dammar’ da dai sauransu birjik.
Idan haka al’amarin yake, abin da ya kamata a yi shi ne a gaggauta yi wa Harshen Hausa gata ta hanyar kafa cibiyar kare harshen Hausa ta kasa domin a daidaita tsari da zubin rubutun Hausa.
Wadanda suka nazarci harshen Hausa suna sane da ginshikai biyu sarai 1. Nahawu 2. Adabi, a saboda haka ba zai kasance azanci ba idan aka zo ana sukar juna cikin rashin tsari (at random) ko kara-zube ba tare da ana kawo ka’idar Nahawu ko rabe-raben Adabi ba.
A ganina abin da ya haifar da sukar-lamirin shi ne daukar Hausa a matsayin harshen Hausa kawai a maimakon harshe (Language) daga cikin manyan harsunan da ake nazarin su a dukkan matakan karatu (Firamare– Jami’a) wanda ya faro daga babbaku (Phonetics) farfaru (Phonology) Tasarifi (Morphology) ginuwar magana (Syntad) ma’anonin lafazi (Semantics), ma’ana, duk harshen da ya kai magariyar tukewa a da’ira ta nazari dole ne a bi wadannan matakai wajen tabbatar da shi.
A nan nake ganin babban dalilin wannan sukar-lamirin (Criticism) shi ne janye manhajar koyar da Hausa a Jami’o’inmu da aka yi maimakon koyar da Hausa a gwame da Turanci (Bi-lingual) sai aka bullo da koyar da Hausa da Hausa (Mono-lingual) wanda a gaskiya hakan shi ya raunana nazarin harshen inda har ta kai daliban Hausar kan yi biyu babu (babu Hausar babu Turanci).
Maganin wannan muhawara shi ne jami’o’inmu su karbi jan ragamar shirya taron kasa domin daidaita tsarin rubuta harshe (Orthography) tare da dabbaka kudurin taron duniya kan rubutun Hausa da aka yi a Bamako (Mali) mai taken ‘Bamako Conference 1963’.
Wassalam
Aliyu Umar Mataimakin Edita na Jaridar Ma’aiktar Yada LAbarai ta Jihar KanoTsohon Editan Jaridar Albishir da aka rika bugawa a Kamfanin Buga jaridu na Triumph Publishing Company, Kano.