Gyaran kundin mulki: Kar dai a yi gyaran gangar Azbinawa

Shugaban Kwamitin gyaran kundin tsarin mulki (CRC), Sanata Ike Ekweremadu, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, ya mika wa majalisar rahoton kwamitinsa game da ra’ayoyin jama’a da aka gangando daga tarurrukan da majalisar dattijan ta yi a shiyyoyin kasar nan guda shida a watannin baya, don jin ra’ayoyin jama’a bisa batutuwan da aka […]

Gyaran kundin mulki: Kar dai a yi gyaran gangar Azbinawa
Gyaran kundin mulki: Kar dai a yi gyaran gangar Azbinawa

Shugaban Kwamitin gyaran kundin tsarin mulki (CRC), Sanata Ike Ekweremadu, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, ya mika wa majalisar rahoton kwamitinsa game da ra’ayoyin jama’a da aka gangando daga tarurrukan da majalisar dattijan ta yi a shiyyoyin kasar nan guda shida a watannin baya, don jin ra’ayoyin jama’a bisa batutuwan da aka tsara don gyara su a cikin kundin tsarin mulkin 1999. Ita ma majalisar wakilai nan gaba za ta gabatar da nata rahoton dangane da yadda jama’a suka yi muhawara, a mazabun wakilanta guda 360, kan batutuwan da ake son gyarawa a  kundin tsarin mulkin.
Daga cikin abubuwan da rahoton Majalisar Dattijan ya kunsa, wanda kuma nan ba da dadewa ba za a fara tafka muhawara a kan su  akwai batun kayyade wa’adin shugaban kasa da na gwamnoni da kuma mataimakansu zuwa shekaru shida-shida, daga nan kuma ba kari. Haka kuma rahoton ya amince da bai wa kananan hukumomi iznin cin gashin kansu, ya kuma yi watsi da batun kirkiro sababbin jihohi. Babu shakka wadannan muhimman batutuwa ne da suka dade suna ci wa jama’ar kasar nan tuwo a kwarya, kuma ko ba a fada ba dattijan majalisa za su tayar da hakarkari wajen tafka muhawara mai zafi, game da su har da kumfar baki.
To amma sai dai shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton Majalisar Dattijai game da gyararrakin za su sha bamban da wadanda Majalisar Wakilai za ta gabatar. Idan har aka samu wani sabani kan wani batu guda  sai a yi watsi da shi, batun gyara ya sha ruwa ke nan. Akwai alamu cewa ita Majalisar Wakilai ba ta amince da wannan batu ba a nata rahoton da za ta gabatar nan gaba ba.Wajibi ne bakunan majalisun biyu su daidaitu kan al’amuran da ake son yin gyaran kafin a zagaya da su zuwa ga jihohin tarayya guda 36 wadanda ake son 24 daga cikinsu su amince da  kowane batu kafin ya zamanto doka. Alal misali batun kirkiro sababbin jihohi abu ne da jama’a suka dade suna hankoron wanzuwarsa, domin kuwa yin haka zai hanzarta raya yankunan da kuma bunkasar tattalin arzikin jama’arsu, sa’annan kuma zai kawo karshen wahalhalu da tashin-tashinar da ke wakana tsakanin mazauna jihohin da suke so a tsattsaga su don kowa ya kama gabansa, a samu sukunin zaman lumana da kwanciyar hankali.
A yanzu haka dai jama’a sun kagara don ganin an ba kananan hukumomi ikon cin gashin kansu, kuma bisa ga dukkan alamu majalisun kasa za su zartar da wannan bukatar. To ba nan gizo ke saka ba, majalisun na iya amincewa, majalisun jihohi kuma na iya fandarewa, su ki yarjewa da haka, domin suna gani za a kawar da ikon da suke da shi na kula da gudanar da harkokin kananan hukumomi da kuma yadda suke sarrafa kudadensu kamar da. Baicin haka nan kuma majalisun na iya mika kawunansu  ga borin gwamnonin jihohinsu don ya hau, domin kuwa ba za su so a ce an daina yi wa shugaban kananan hukumomi inkiya da kudadensu ta hannun gwamnonin jihohi ba.
To bar ta wannan. Babbar magana game da haka ita ce ta kayyade wa’adin zababbun shugabanni a jihohi da kuma tarayya zuwa falle guda  na shekaru shida. Wannan magana ce da Shugaba Jonathan ya fara takalo ta tun ma kafin majalisun kasa su yunkura don fara daukar matakan yin gyara ga kundin tsarin mulki, watakila don yana son tsawaita zamanin mulkinsa. To, biri ya yi kama da mutum, domin kuwa wasu na ganin cewa wannan batu ne da aka shigar da shi cikin rahoton Majalisar Dattijai ta bayan gida domin kawai a shafa wa jama’a mai a baki, har ta kai sun matsa wa wakilansu amincewa da haka don a kai ga biyan wata boyayyiyar manufa can ta daban wacce za ta iya ba wadannan shugabanni damar shantakewa bisa mulki na wani tsawon lokaci. Masu goyon bayan wannan tsari na cewa haka shi ne mafi a’ala wajen magance kataniya da kata-katar siyasa a kasar nan, domin kuwa babu abin da ke kawo yamutsi da rigingimu a lokutan zabe, ko kawar da hankalin zababbun shugabanni daga ayyukansu, kamar kokarin zarcewa a karo na biyu, kuma idan aka kayyade wa’adin zuwa karo guda za a yi ban-kwana da su har jaririyar dimokuradiyyar kasar nan ta samu sukunin tsayawa bisa kafafunta.
Masu adawa da tsarin kuma na ganin kunshi ne a baraka ake son yi, domin ba abin da wa’adin mulki, fallan daya, zai haifar illa karfafa zukatan wasu zababbun shugabanni wajen satar dukiyar jama’a domin sun san daga karshe za su tsira da na bakinsu ne, ba za su sake waiwayar jama’a don neman kuri’unsu ba, tun da za su fita da fitarsu. Sa’annan kuma wasu na tsoron cewa hakan zai takurawa talakawa hakurewa da shugaban da suka kosa da shi, walau saboda lusarancin da ha’incinsa ko rashin sanin makamar aiki, tun da dai ba za su iya kawar da shi ba cikin gajeren lokaci.
Babban abin da ya kamata a yi la’akari da shi game da aikin gyaran kundi da ‘yan majalisa ke yi shi ne ba safai ake yin haka ba sai idan akwai wani kwakkwaran dalili. A shekarar 2010 an yi ‘yan gyararraki cikin kundin tsarin mulki don kawar da sarkakiya game da harkokin zabe, ga shi kuma a wannan karon ana son yin gyararraki masu yawan gaske wadanda za su kayatar da wasu, su kuma kasa gamsar da wasu. Babu wani dalilin da zai sa nan gaba kadan wasu ba za su sake neman a yi wasu gyararrakin ba, ganin cewa an huda, an ga jini. Fatanmu a nan shi ne kada dai a yi gyaran gangar Azbinawa.