Gyaran Kundin Tsarin Mulki

Kwamitin gyaran tsarin mulki na Majalisar dattawa ya bayar da shawarar a koma wa hukumar zabe ta kasa (INEC) da hakkin gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a kasar nan. Kamar yadda wata majiya da ke cikin kwamitin ta shaida wa Aminiya.Shugaban wata karamar hukumar a jihar Neja wanda ba ya son a ambaci sunansa,ya bayyana […]

Gyaran Kundin Tsarin Mulki
Gyaran Kundin Tsarin Mulki

Kwamitin gyaran tsarin mulki na Majalisar dattawa ya bayar da shawarar a koma wa hukumar zabe ta kasa (INEC) da hakkin gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a kasar nan. Kamar yadda wata majiya da ke cikin kwamitin ta shaida wa Aminiya.
Shugaban wata karamar hukumar a jihar Neja wanda ba ya son a ambaci sunansa,ya bayyana cewa wannan shawarar abu ne da yake maraba da shi, bisa la’akari da cewa abin da suka ga ya fi dacewa a yi musu ke nan  a lokacin da suka bayyana  ra’ayoyinsu a lokacin taron sauraron ra’ayoyin jama’a game da gyaran kundin tsarin mulkin da aka yi bara .
Shugaban ya kara da cewa, muddin aka yi musu yadda suke so za a zauna lafiya,idan  kuma aka yi akasin abin da suke so,sakamakon ba zai zama da dadi ba.
Ya jaddada cewa wannan matakin zai yi matukar tasiri don zai sa jama’an da ke ganin magudi zai kai su mukaman kujerun Shugaban karamar hukuma,ko na kansila su sake tunani, ganin  yadda jama’a ke kara wayo tare da nazarin irin wainar da ake toya wa a al’amuran da suka shafe su.  
Haka kuma Aminiya ta gano cewa kwamitin majalisar dattawan wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu yake shugabanta, ya kuma amince a rushe tsarin nan na asusun hadaka tsakanin jihohi da kananan hukumomi da ake ta cece-ku-ce a kansa.
Kwamitin kuma ya amince a haramta bai wa duk wata karamar hukumar da ba zababbun shugabanni ne suke gudanar da ita ba kudin shigar da ya kamata ta samu. Inji majiyar tamu.
Gwamnoni dai sun dade suna jayayya da wadannan shawarwarin guda biyu da suka shafi kananan hukumomi, wanda ya sanya ake tunanin za su kalubalanci wadannan shawarwarin inda maganar ta isa majalisun jihohinsu domin samun amincewarsu.
Amma mafi yawan mutanen da suka bayyana ra’ayoyinsu a lokacin sauraron jin ra’ayin jama’a da majalisun tarayya guda biyu suka gudanar suna goyon bayan bai wa kananan hukumomi ‘yancin kashe kudadensu ba tare da katsalandan ba da kuma rushe hukumomin zabe mallakar jihohi, wadanda ake ganin gwamnoni ne ke juya akalarsu.
Haka kuma Kwamitin ya amince da tsarin lokaci guda na shekara shida ga shugaban kasa da gwamnoni a zabubbukan da za a gudanar nan gaba. Sai dai kwamitin ya bukaci kada shugaban kasa mai ci yanzu ya amfana daga tsarin.
Tsarin gudanar da mulki sau daya ga shugaban kasa al’amari ne da ya jawo mahawara mai zafi tun a shekarar 2005 lokacin da aka yi watsi da yunkurin yin gyara ga tsarin mulki gaba dayansa, a sakamakon tsoron da ake ji cewa tsohon shugaban kasa Obasanjo zai yi amfani da hakan ne domin ya tsawaita wa’adin mulkinsa.
‘Yan majalisar dai za su yi gyaran a bangarori da dama na tsarin mulki ne, kuma sun ware watan Yuli a matsayin lokacin da za su kammala aikin nasu.
Kamar yadda shugaban kwamitin ya nuna, kwamitin nasu zai gabatar wa majalisar da rahotonsa a wannan makon domin amincewarsta, haka su ma ‘yan majalisar wakilai za a bukaci amincewarsu.
Ya yi fatan majalisar  ‘’za ta hanzarta dubawa kuma ta amince domin su samu damar cimma wa’adin da aka diba na watan Yuli, ko da za a wuce dai ba zai zama an dauki lokaci mai yawa ba, babu shakka mun bi tsarin lokacin gudanar da aikin namu na gyaran tsarin mulkin sau da kafa.’’ Inji shi.
Sai dai kuma mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce wannan rahoton nasu ba shi ne matsayin majalisa ba, ‘duk shawarar da muka yanke sai mun gabatar wa ‘yan uwanmu a majalisa wadanda za su amince bayan sun tuntubi mazabunsu da kuma sauran daukacin ‘yan Najeriya’’. Inji shi.
Haka kuma Sanata Ike Ekweremadu ya bayyana cewa, duk cikin masu bukatar kirkiro sababbin jihohi babu wadanda suka cika ka’idojin da sashi na 8, karamin sashi na (1) na tsarin mulkin shekarar 1999 da aka yi wa gyara ya tanada.
Ya ce, kwamitin nasu ya karbi bukatar kirkiro jihohi fiye da hamsin daga bangarori daban-daban na kasar nan, ‘’amma mutane sun dauka za su zo Abuja ne kawai su mika bukatarsu, ita kuma majalisa ta tattauna, daga nan sai kawai ta bayyana jihohi kaza da kaza sun samu hayewa, alhali abin ba haka yake ba.’’
‘’Idan mun karbi wata bakata game sabuwar jiha, dole ne, kamar yadda tsarin mulki ya tanada, sai kashi biyu bisa uku na kananan hukumonin jihar da za a fitar da sabuwar jihar daga cikinta sun sanya hannu, wadanda za su kunshi kansilolo da shugabannin kananan hukumomi zababbu, domin tsarin bai san da shugabannin riko ba.’’
‘’Haka kuma dole a samu sanya hannun kasha biyu bisa uku na ‘yan majalisar jihar da abun ya shafa. Sannan kuma a samu sanya hannun kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisun majalisun tarayya da ke jihar. Amma abin da ya faru yanzu shi ne, sarakunanmu na gargajiya sune saboda tsananin kaunar da suke yi wa jama’arsu suka sanya hannu a bukatun neman jihohin suka kawo Abuja ba tare da duba tanadin da tsarin mulkin ya yi ba.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’ba su ne ya kamata su sanya hannu ba, ‘yan majalisu ne wadanda suke cikin majalisa ba tsofaffi ba za su sanya hannu, kamar yadda na fahimta.’’
‘’Wannan shi ne daya daga cikin ka’idojin da masu bukatar sabuwar jiha ba su cika ba, domin wannan shi ne ya yi mana tarnaki a aikinmu, muna goyon kara jihohi amma dole ne mu bi ka’idar da tsarin mulki ya shimfida, wanda mafi yawan mutane suka kasa cikawa. Wannan shi ne matsayinmu.’’ Inji mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu.