Gyaran magudanar soyayya
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili da fatar Allah Madaukakin Sarki Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. A yau insha Allah za mu yi bayani ne kan hanyoyin da ma’aurata z asu bi don gyara magudanar soyayyar auratayyarsu. Da fatar Allah Ya sa wannan […]
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili da fatar Allah Madaukakin Sarki Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. A yau insha Allah za mu yi bayani ne kan hanyoyin da ma’aurata z asu bi don gyara magudanar soyayyar auratayyarsu. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Yanayin soyayya:
Da farko yana da kyau ma’aurata su fahimci cewa soyayya ita ce babban makasudin kasancewarsu ma’auratan juna; soyayya ita ce muhallin auratayya; in ba soyayya a cikin rayuwar aure, to auren nan zai zama fanko ba rahama a cikinsa; haka kuma soyayya ita ce dadin auratayya, auren da ba soyayya a cikinsa za ka same shi lami ba dandano a cikinsa, ko kuma a samu dandanonsa mai daci ko hamami.
Soyayya kalma ce ta aiki mai gudana wanda ake cikin yin sa a koyaushe ba dakatawa; haka manyan sinadaran da suka gina soyayya; kaunatayya da kulawa dukkansu aikatau ne masu gudana. Al’amurra da dama na faruwa a cikin rayuwar aure, wadanda a hankali suna taruwa har su yi yawa su lullube soyayya kuma su cushe magudanarta, sai ta tsaya cak ba ta gudana. Duk soyayyar da ba ta gudana kuwa to kamar babu ita ce, domin ma’aurata ba su amfana da ita. Don haka sai ma’aurata su bi wadannan hanyoyin don gano matsalolin da suka taushe soyayyarsu har ya zamana ba ta gudana.
Bincike:
Ba a iya maganin matsala har sai an gano yanayinta da abin da ke haifar da ita; don samun saukin gyara magudanar soyayya, sai ma’auarata su binciki kansu game da soyayyarsu kuma su yi kyakykyawan nazari kan wasu al’amura da suka shafi soyayyarsu da kuma gano hanyoyin magance wadannan matsalolin.
Ga wasu jerin tambayoyi da ma’aurata za su amsa don gane inda soyayyarsu ke da tangarda da kuma abin da ya haifar da wannan tangardar:
Ina son mijina/matata kuwa?
Me ya sa nake son sa/ta?
Yaushe na fara son sa/ta?
Shin son yana karuwa ne ko raguwa?
Me ya sa shi karuwa/raguwa?
Akwai wani laifi da ya sa na rage son sa/ta?
Ina ganin kima da darajarsa/ta kuwa?
Akwai wani laifi da ya yi/ta yi mini da ya sa ban ganin kimarsa/ta kamar da?
In na gan sa/ta yaya nake ji, dadi da murna; bakin ciki da haushi; ko ba na jin komai?
Ina bayyanar da soyayya ta gare shi/ta kuwa: In amsar ‘eh’ ce; ta wadanne irin hanyoyi ne; in kuma a’a, me ya sa?
Shin mijina/matata na sona kuwa?
Ta wadanne hanyoyi nake gane yana/tana sona?
In kuwa bai sona/ba ta sona, me ya sa?
Yaushe nake jin ya/ta daina sona?
Wani laifi na yi da ya sa ya/ta daina sona?
Yaya zan ji yau a wayi gari a ce mijina/matata ba ya/ba ta duniya?
Ma’aurata na iya kara wasu tambayoyin da suka ga sun dace da yanayinsu.
Gyaran fuska:
Amsa wadancan tambayoyi da ke sama zai ba ma’aurata hoton irin yanayin da soyayyarsu take ciki, zai sa su fahimci matsalolin da suka cushe magudanar soyayyarsu; don haka sai su samu takarda su rubuta dukkan inda suke ganin akwai wata matsala, su binciko abin da ke haifar da wannan matsala sannan su yi nazarin hanyar da suke ganin zai kawar masu da wannan matsala; in matsalar daya ne daga cikinsu ke haifar da ita, sai ya yi aniyar yin dukkan kokari don ganin ya kawar da wannan matsala; in ko su duka kowa na da hannu cikin matsalar, sai su duka su yi dukkan kokarin magance wannan matsala.
Habaka soyayya:
Bayan ma’aurata sun gano matsalolin da suka cushe magudanar soyayyarsu kuma sun magance wannan matsala, daga nan sai su yi kokarin yin abubuwa da za su habaka soyayyarsu ta kara yawa da inganci. Ta hanyar gano sababbin hanyoyin dadada wa da faranta wa juna rai; ta hanyar yin kokarin kara yawan lokacin kasancewa tare ba wai dole sai lokacin barci kadai ba; ta hanyar yin sabon dashen kauna cikin zuciyar juna; ta hanyar yawan sabunta kaunatayyarsu da soyayyarsu a kai-a kai; ta hanyar cakuda so da kauna da romansiyya cikin ibadar aurensu; da duk wasu hanyoyin da suke ganin za su habaka tare da kara rayar da soyayyarsu cikin zuciyar juna; inshaAllah bayani na zuwa kan kyawawan hanyoyin da ma’aurata za su bi wajen bayyanar da soyayya ga junansu.
Ma’aurata sai a mike tsaye, a kuma dage a yi dukkan kokarin da ya kamata don yin gyara ga muhallin auratayya; kar a yi ta zaman hakuri ana rayuwar auratayya kamas ba soyayya; duk wani abu da ke hana bayyanar da soyayyar ga juna ya kamata a yi fatali da shi domin ba amfanin da yake ga rayauwar aurenku, kuma ko da yana yi din, tabbas bayyanar da soyayyar ga juna ta fi zama alfanu. Ku tuna, rayukanmu duka ba a hannunmu suke ba, ba wanda ya san ranar mutuwarsa, mutuwa na iya dauke abokin aurenku, ko ku a kodayaushe, sannan ne za ku rika da- na- sani na yi masa ko mata kaza? Da fatan Allah, wanda zukatan dukkan mai rai ke karkashin ikonSa, wanda Ke shamakancewa tsakanin mutum da zuciyarsa, Ya cika zuciyar dukkan ma’aurata da so, kauna, kulawa da sha’awar juna, amin.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba insha Allah. Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsSa koyaushe, amin.