Gyaran Najeriya: Ba dabo Buhari zai yi ba – Ben Bruce

Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas a Majalisar Dattawa Sanata Ben Murray Bruce, ya ce ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa Buhari mutum ne suka zaba ya shugabance su ba mai yin dabo ba ne, don haka akwai bukatar su nuna hakuri da tsohon shugaban mulkin sojan. Sanatan ya kuma yi tir da wadanda […]

Gyaran Najeriya: Ba dabo Buhari zai yi ba – Ben Bruce
Gyaran Najeriya: Ba dabo Buhari zai yi ba – Ben Bruce

Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas a Majalisar Dattawa Sanata Ben Murray Bruce, ya ce ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa Buhari mutum ne suka zaba ya shugabance su ba mai yin dabo ba ne, don haka akwai bukatar su nuna hakuri da tsohon shugaban mulkin sojan.

Sanatan ya kuma yi tir da wadanda suke sanya siyasa a cikin hare-hare na bayan nan da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a sassan kasar nan.
Sanata Ben Bruce, wanda aka zaba a karkashin Jam’iyyar PDP kuma yake wakiltar yankin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce a shafinsa na Tweeter cewa, shi yadda ya fahimci adawar siyasa ba ita ce a rika suka da zagin Buhari ko Jam’iyyar APC mai mulki ba, maimakon haka adawa ita ce a samo hanyoyin da yin kaimi wajen inganta rayuwar al’ummar Najeriya.
Wasu daga cikin bayanan da ya rubuta a shafin nasa sun hada da: “Allah wadan duk wanda ke son siyasantar da hare-aren ta’addanci na baya-bayan nan. Buhari yana bukatar goyon bayanmu domin ya kawar da ta’addanci, kuma wajibi ne a kanmu mu goya masa baya.”
Sai kuma “Yadda na dauki adawa ba ita ce a rika bata suna Buhari ko APC ba. Adawa a wurina a nemo maslaha da bayar da shawarwarin da za su inganta jin dadin jama’ar Najeriya.”
Sai ya kare da cewa: Har wa yau ina nanata cewa, kasa ba ta bunkasa cikin dare daya. Ku ba Shugaban kasa Buhari lokaci. ’Yan Najeriya sun zabi mutum ne ba dan dabo ba.”