Gyaran Najeriya: Shin ta ina za a faro?
Yau kuma MALAM ANAS SAMINU JA’EN (07033882307) [email protected] <mailto:[email protected]>; ya yi tsokaci ne game da sabuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ba shugaban da sauran al’ummar kasa shawarwarin yadda za a bullo wa al’amuran da suka sukurkuce a kasa. Ga abin da suke cewa: Idan ’yan Najeriya za su tuna, duka kasashen da muke […]
Yau kuma MALAM ANAS SAMINU JA’EN (07033882307) [email protected] <mailto:[email protected]>; ya yi tsokaci ne game da sabuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ba shugaban da sauran al’ummar kasa shawarwarin yadda za a bullo wa al’amuran da suka sukurkuce a kasa. Ga abin da suke cewa:
Idan ’yan Najeriya za su tuna, duka kasashen da muke kira sa’aninmu, irin su Brazil, Indiya da sauransu, ba wani abu ne ya sa suka yi mana zarra ba illa tsayayyen shugabanci da suke da shi kuma mai manufa.
Tabbas idan za a samu kasa kamar tamu Najeriya kuma za a samu mutane miliyan dari da tamanin amma kuma ya zamanto babu shugaba wanda yake yana da tsayayyar magana guda daya to kun ga ba zai taba daukar kasar da muhimmanci ba.
Duk da na san wasu za su ce a irin tafiyar da ake yi a Najeriya, duba da dimbin bashin da aka ciyo mata za a dade ana gabzawa. Ga farashin mai ya fadi kasa, babu wutar lantarki da sauran abubuwa da dama. To a nan nake cewa da duk wani dan kasa nagari mai kishin talakawa, ya sha kuruminsa. a ba wannan sabuwar gwamnatin wata shida shida, duk dan kasar nan zai yi dariya saboda duk wadancan matsalolin za su kau da yardar Allah.
Haka kuma kowa ya san a baya an yi shugabanci mara alkibla. Ya za a yi a ce kasa kamar Najeriya mai miliyoyin mutane wai a ce an kashe dala biliyan 20 wajen samar wa kasar wuta kuma babban abin takaici shi ne, wasu sassan kasar sai a shafe wata da watanni ba su da wutar lantarkin, har lokacin da aka ce Shugaba Jonathan zai mika wa Muhammad Buhari ragamar kasar, sannan ma babu wutar lantarkin a duk sassan kasar baki daya.
Kowa ya san abun da ya kawo wadannan abubuwa shi ne sace-sacen da ake yi a kasar nan babu-ji-babu-gani, yayin da duk aka ce an toshe hanyoyin da ake yin sace-sacen da wasu mutane kalilan da suka hana kasar nan sakat ke yi, za a iya samu sa’ida. Yanzu misali kamar maganar wuta, ai wasu shafaffu da mai ne suke fasa bututun da yake kawo gas, ya za a yi a ce muna da sojoji da ’yan sanda, ana irin wadannan rashin mutuncin. Saboda irin rashin shugabancin da muka rasa a baya, sai a jefa miliyoyin mutane cikin wahala ana tafiyar da kasa kamar babu gwamnati
Tabbas matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka a ranar da ya shiga ofis, inda ya ce umurci hafsoshin tsaro su koma Arewa maso gabas gaba daya, ya dace. Ni ba ma’aikacin tsaro ba ne kuma ba masanin harkokin tsaro ba ne amma wannan mataki ya dace. Amma da can baya, wadanda suke yaki daban, wadanda suke bayar da umarni daban kuma suna Abuja; su kuwa kananan sojojin suna can suna fafatawa da masu tayar da kayar baya.
Kuma a nan sai dai mu ce alhamdu lillahi, babu abun da za mu ce da sabon shugaba sai godiya. Idan ‘yan Najeriya ba su manta ba, cikin shekaru 31 da suka wuce Muhammad Buhari shi ne Shugaban kasar Najeriya kuma shugaban askarawan ne. Don haka babu wanda zai ce maka ya yi wani aiki da ake zarginsa da na sata ko daure wa wasu gindi, balle ma ka ce yana da yara mabiyansa. Kuma ya san aikin tsaro ya fara aikin tsaro ya gama har kawo yau, haka ce ta sa duk dan kasa da ma wasu kasashen duniya ake ganinsa mai magana daya. Duba da irin kwarewarsa da kuma jajircewarsa a kowane fanni. Na san Buhari ba zai taba cin amanar ’yan kasa ba, domin zai yi amfani da iya abin da ya sani wajen kawo ci gaba a wannan kasa tamu. Na san idan aka ce tsaro, zai nemo irin dakarun tsaron da ya sani, wadanda ba za su ci amanar kasa ba.
kasar nan a yanzu, babban Abun da yake damunta shi ne matsalar Boko Haram a yankin Arewaci. Su kuma Kudanci akwai sace-sacen al’umma. To a nan nake cewa tsarin irin mulkin da, da kuma wannan akwai bambanci sosai. Adadin mutane da suka bar aikinsu kara-zube a banza saboda shugabanni sun nuna musu yadda ake yin satar dukiyar talakawa, sannan jama’ar kasa da dama suna ganin cewar Buhari idan ya zo zai kori mutane a wannan. Ba haka yake ba, duk da ban san ya zai yi ba, ina mai tabbatar muku cewa idan aka yi garanbawul a kowace ma’aikata da take fadin kasar nan, to su kansu sun san gyara ya zo kuma idan aka ce mutun ya yi abun a ake yi, da ina mai tabbatar muku ko wurin ba zai tunkara ba.
A nan ne kowa zai yaba da irin abin da sabon shugaba zai aiwatar domin za a guji cin hanci da rashawa. A gaskiya a nan nake ganin a maida harkar matsalar man fetur. Haka kuma Shugaban kasa sai ya yi taka tsantsan wajen zabo irin mutanen da zai yi aiki da su, saboda duk wadanda suka zagaye shi suna sunne-sunne, to fa ba su ba ne kasar nan take bukata. Akwai mutane nagari, wadanda azzalumai sun hana su motsi. Irinsu ya kamata a je a zakulo su, domin a kawo bambanci a cikin wannan siyasar da muke ciki. Ta nan ne za a zabo nagartattu, wadanda za su taimaka masa.
Yanzu abun da ya kamata a duba shi ne irin cin hancin da ake yi a bangaran man fetur, musamman kan tallafin da ake bayarwa na fetur. Shi kansa tallafin da ake bayarwa ya zama wajibi a zo a cire shi, amman kafin a cire din a fara gyara matatun man da muke da su a kasar nan. Abun da masana a kasar nan ke cewa, kashi 16 ne ke yin aiki a cikin 100 Wanda ya dace a ce suna aiki kashi 60 cikin 100. Sannan a zo a gina wasu sababbin matatun man, wadanda za su rika fitar da mai kamar ganga dubu dari uku da hamsin a rana daya. Lallai za a iya yin wannan aikin cikin watanni shida masu zuwa.
Babban abun da zan ce a nan shi ne, dole mu tashi tsaye mu taya sabon Shugaban kasa da addu’a, domin barnar da aka yi a kasar nan tana da yawa kuma an debi wasu shekaru da dama ana yin satar. Al’ummar Najeriya suna ta tunanin za a yi gyara a kan barnar amman ina dada nusar da ’yan uwa cewa a yi hakuri, domin idan ana son canji to dole fa a debi wasu lokuta. Don canji lokaci daya ba zai samu ba amma inda na ji dadi shi ne, Muhammad Buhari an shaide shi wajen gaskiya da rikon amana kuma ya ci alwashin cewa duk yadda za a yi zai yi kokarin ganin an kawo gyara a kasar nan. Don haka ya kamata mu ’yan Najeriya mu ba shi kyakkyawar gudummawa dari-bisa-dari.