Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja
Kamfanin ya ce gyaran ya zama dole ne domin inganta wutar lantarki a yankunan.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ya sanar da fara yin gyare-gyare wanda ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A cewar mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, injiniyoyin kamfanin za su gudanar da gyare-gyare a tashoshi biyu na rarraba wutar a ƙarshen mako.
- Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa
- Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024
Ya ce a ranar Asabar, 28 ga watan Disamba, daga ƙarfe 9 na safe zuwa 1 na rana, za a yi gyare-gyare a tashar wutar lantarki ta Gwagwalada.
A cewarsa hakan zai shafi wutar lantarkin Gwagwalada da kewaye.
A ranar Lahadi, 29 ga watan Disamba, daga karfe 9 na safe zuwa 10 na dare, za a yi aiki a tashar wutar lantarki ta Kukwaba, wanda zai janyo ɗaukewar wuta a Wuye, yankin EFCC, Coca-Cola, tashar jirgin ƙasa ta Idu, Citec, da kuma Life Camp.
TCN, ya nemi afuwa kan wannan matsala, tare da bayyana cewa gyare-gyaren sun zama dole domin inganta samar da wutar lantarki.