Gyaran tsarin mulki ne kadai zai taimaka wa Buhari wajen yaki da barayin gwamnati – Farfesa Dadari
Wani malami a Sashin Binciken Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Farfesa Salihu Adamu Dadari ya yi kira ga wakilan majalisun dokoki Najeriya da sauran al’ummarta kan su tashi tsaye, domin ganin gyara kundin tsarin mulkin Najeriya, domin a taimaka wa Shugaban kasa Muhammad […]
Wani malami a Sashin Binciken Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Farfesa Salihu Adamu Dadari ya yi kira ga wakilan majalisun dokoki Najeriya da sauran al’ummarta kan su tashi tsaye, domin ganin gyara kundin tsarin mulkin Najeriya, domin a taimaka wa Shugaban kasa Muhammad Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa da yake a kasar nan.
Farfesa Salihu Adamu Dadari ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce yin hakan ne kadai zai taimaka wa gwamnatin Buhari kan wannan kokari da take yi, na yaki da cin hanci.
Ya ce a lokacin da aka yi wannan kundin tsarin mulki da ake amfani da shi yanzu ba a samun masu satar kudin gwamnati da yawa irin na zamanin gwamnatocin da suka gabata ba, don haka babu dokokin da aka tanada domin hukunta masu irin wadannan laifuffuka.
“A yau an wayi gari sai mutum daya ya saci Naira miliyan dubu. Kuma idan ka kai wannan mutum kotu, za a ce babu hukunci mai tsanani da aka tanadar masa a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. Saboda haka ake amfani da alkalai da lauyoyi wajen kubuta daga wadannan miyagun laifaffuka da suka aikata. Don haka ya zama wajibi mu hada kai da wakilan majalisunmu da kowa da kowa, a samu a gyara kundin tsarin mulkin kasar nan, a samar da dokoki masu tsanani da za a rika hukunta irin wadannan barayi, domin gwamnatin Buhari ta ji dadin tunkarar wannan bala’i da ya dabaibaiye Najeriya,” inji shi.
Farfesa Dadari ya yaba wa gwamnatin Buhari kan matakan bunkasa harkokin noma da ta dauka, inda ya ce matakai ne masu kyau. Ya ce a cikin matakan akwai maganar farfado da noman auduga ta yadda za a samu a farfado da masaku, wadanda akalla za su samar wa ’yan Najeriya kimanin miliyan 50 ayyukan yi. “Har ila yau gwamnati ta ce za ta inganta noman shinkafa a kasar nan, domin bai kamata a rika kawo shinkafa daga kasashen waje ba, wadda ba ta kai wadda muke nomawa inganci ba,” inji shi.
Ya ce manyan kasashen duniya irin su Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da China da Kanada ba su yi wani tasiri ba, sai da suka rungumi aikin noma.
Sai ya yi kira ga al’ummar Najeriya su ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’a tare da ba ta goyon baya domin ta samu nasarar kudirorin da ta sanya a gaba.