Gyaran wasu kura-kurai a wajen yin kwalliya
A wasu lokuta mutane kan aikata kura-kurai da dama wajen tsarin kwalliyar fuskarsu. Yayin da wadansu kan yi haka saboda sauri, wadansu kuma rashin sanin yadda ya kamata su yi kwalliyar ce ke jawo musu haka. Koma wane dalili ke jawo haka, ya kamata mace ta rika tanadar wa kanta isasshen lokaci don yin kwalliya, hakan […]
A wasu lokuta mutane kan aikata kura-kurai da dama wajen tsarin kwalliyar fuskarsu. Yayin da wadansu kan yi haka saboda sauri, wadansu kuma rashin sanin yadda ya kamata su yi kwalliyar ce ke jawo musu haka.
Koma wane dalili ke jawo haka, ya kamata mace ta rika tanadar wa kanta isasshen lokaci don yin kwalliya, hakan ba zai yiwu ba sai kin zama mai tsara lokacinki a kullum. Kuma dole ki nemi madubi mai kyau. Abu na karshe kullum ki rika neman shawarar kwararru. Kula da yadda za a tsara kwalliya abu ne da ya zama dole, musamman a wannan zamani da kowace mace ke kokarin a gan ta kamar budurwa.
Ga kadan daga cikin kura-kuran da yadda za a gyara su:
1. Mata da yawa kan shafa hoda ba tare da la’akari da zabar wacce za ta dace da fatarsu ba. Yawanci jar hoda takan yi wa fata mai duhu kyau, amma ita din ma dole sai mace ta nemi lambar da za ta yi daidai da fatarta. Idan za ki shafa hodar ki shafa ta wajen kasan idonki da wuraren hancinki zuwa kumatunki sannan sai ki dan goga a saman goshinki. Amma idan kina shafawa a kasan idonki ki kula da kyau don kada hodar ta taba miki gashin ido. Akwai bukatar ki tabbatar kin dirje ta yadda za ta bi fatar fuskarki sosai. Kada ki bari ta yi miki dabbare-dabbare.
2. Mata da yawa ba su fara la’akari da yanayin gashin girarsu mai yawa ne ko kadan kafin su kai ga zizara jagira. Za ki fara da zabar jagirar da za ta dace da gashin girarki. Idan har gashin girarki mai yawa ne kamata ya yi ki gyara shi ta hanyar taje shi ya kwanta tare da zizara ’yar jagira kadan a kai. Haka wadansu sukan yi kuskure wajen rage yawan gashin girarsu, inda suke aske fiye da yadda ya kamata. Idan har za ki gyara gashin girarki ki yi shi da natsuwa ko ki nemi wanda kika san ya kware ya yi miki.
3. Mata da yawa kan yi kuskuren zaben launin da ya dace su shafa idan an zo batun kwalliyar kan ido. Kuma wadansu ba tare da sanin abin da ya dace su yi ba sukan shafa kwalliyar har ta yi yawa a kan idon. Abin damuwar shi ne idan har kwalliyar ta yi yawa ba za a dauki lokaci ba za ta fara zazzagowa ta zama wani abu daban. Na san wadansu sukan zabi launin da zai yi daidai da suturar da ke jikinsu, amma ki sani ba kowane launin ashado ne don ya yi daidai da launin suturarki za ki sanya kai-tsaye ba. Akwai bukatar idan har kin san launin bai fiye karbarki ba a yi masa hadi da wani launin yadda zai ba da wani launi na daban sannan ya fito da kwalliyarki sosai.
4. Shi ma shafa jambaki da layin da ake ja a kasan lebe suna da nasu tsarin. Kamata ya yi bayan kin shafa jambakin da kika san ya yi daidai da launin jikinki sannan kuma kika shafa shi daga cikin leben yadda ba zai fito waje ba. Idan kika gama sai ki dauko ‘ip liner’ (sunan da ake kiran abin da ake jan layin lebe da shi) wanda zai yi daidai da irin jan bakin da kika shafa sannan ki ja, amma akwai bukatar jan layin ya zama dan siriri yadda ba zai fito ya yi yawa daga wajen lebenki ba.
Kuskuren da wadansu mata ke yi shi ne yadda suke daukar jagira su zane kasan lebansu da ita a maimakon ‘lip liner.’ Mun sani a lokacin da kika shafa yakan yi kyau na awa daya zuwa biyu, amma da ya wuce haka jambakin ya fara fita to kwalliyar za ta canja sunanta zuwa wani abu daban.