Gyare-gyarenmu: Kwalliya na biyan kudin sabulu- Shugaban Hukumar hajji

Tun lokacin da shugaban Hukumar Hajji ta qasa (NAHCON) Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad ya fara aiki. Shugaban ya fito da wasu shirye-shirye guda 15 wadanda ya sanya a gaba, wanda wasu ba za su yiwu ba. Amma cikin shekara biyu da fara aiki, za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu. Wadannan shirye-shiryen sun […]

Gyare-gyarenmu: Kwalliya na biyan kudin sabulu- Shugaban Hukumar hajji


Tun lokacin da shugaban Hukumar Hajji ta qasa (NAHCON) Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad ya fara aiki. Shugaban ya fito da wasu shirye-shirye guda 15 wadanda ya sanya a gaba, wanda wasu ba za su yiwu ba. Amma cikin shekara biyu da fara aiki, za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu. Wadannan shirye-shiryen sun fara samar da ci gaba a duk vangarorin ayyukan lura da mahajjata musamman a hajjin bana.

Rassan hukumar na jihohi da vangarorin gwamnati, duk an tabbatar da cewa suna aiki da qwarewa matuqa, da kuma tabbatar da aiki da cikawa. An gyara vangaran masu kai ziyara domin a samu aiki na qwarai, an zavo kamfanonin jirage masu nagarta kuma ana lura da aikinsu yadda ya kamata domin a tabbatar mahajjata sun samu natsuwa kuma anyi jigilarsu cikin lokaci. Masaukin alhazan a Makka da Madina masu kyau ne ba kamar na da ba domin yanzu mahajjatan suna zauna ne a Otel din Markaziyya a kusa da masallacin Annabi a Madina. Kuma yawancin mahajjata yanzu ana kai su har filin jirgin Yarima Abdul-aziz. Rajistan mahajjata a yanar gizo da takardar shaidar shiga qasa kuma sun taimaka wajen sauqaqe hanyar lura da mahajjta.

Ma’aikatan lafiya na musamman na qasa da aka tura sun sauqaqe harkar kiwon lafiya. Mahajjatan 2017 sun mori harkar sufuri mai sauqi a cikin Qasar Saudiya. Hakanan kuma sauyin da aka samu a vangaren alawus din tafiye-tafiye da na hadaya ya magance cuwacuwar da ke cikin lamarin. Yadda vangaren yada labarai ke aiki cikin tsari yasa ‘yan Najeriya na samun labarin ayyukan hukumar da kuma mahajjata yadda ya kamata. Sannan kuma bugu da qara, ga yadda ake ilimantar da mahajjatan ta kafofin NTA da FRCN. Sannan kuma ana samun ruwan Zamzam cikin sauri.

A lokacin bikin cika shekara 10 da kafa hukumar a Abuja a kwanakin baya, shugaban hukumar ya ce “Ya tabbata cewa bamu kauce ba daga manufofin hukumar, kuma bamu vata wani tsari ba, ko kuma mu kasa ciki tsammanin musulmi saboda yardar da gwamnatin ta nuna da kuma yardar Allah. Ina da tabbacin cewa muna kan hanyar daidai. Shugabanninmu da kuma wadanda muke hada hannu da su sun san cewa muna aiki ne saboda mahajjatan Najeriya”

Hakanan nan kuma, NAHCON ta shiga wani yarjejeniyar hadaka da Hukumar Fadakarwa ta qasa (NOA), da kuma Hukumar hana sha da fataucin miyagun qwayoyi ta qasa (NDLEA) da kuma wasu muhimman hukumomi na gwamnati da kuma masu zaman kansu domin tabbatar da cewa an sauqaqe hajjin.

Tallafin da ake samu daga gwamnatin jihohi abin a yaba ne. jihohin sun kasance suna hada hannun da Hukumar ta qasa domin samar da sauye-sauye masu muhimmanci ga aikin hajji a Najeriya. An gargadi shugabannin hukomomin hajjin na jihohi a kan cin hanci da rashawa, kamar yadda Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya umarci shugaban Hukumar Mukhtar Abdullahi da ya tabbatar ya yaqi cin hanci da rashawa a hukumar. Da wadannan sauye-sauyen da aka samu, mahajjatan Najeriya na samun duk abin da ya kamata su samu a wannan shekarar. Wadannan sababbin tsare-tsaren da aka samu a vangarori da dama na hajji, lallai abin a yaba wa hukumar ne, kuma ya kamata a ci gaba daga inda aka tsaya a hajjin badi.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara