Gyatuma ta kafa tarihi a tseren San Diego
Wata gyatuma mai shekara 91 ta kafa tarihi a wajen gasar tsere ta “Rock ‘n’ Roll” da aka gudanar a San Diego, inda cikin sa’o’i bakwai da mintuna bakwai da dakika 42 ta karade wuri mai nisan mil 26. Wannan tsdohuwa, mai suna Harriette Thompson da ta fito daga North Karolina, ta zama mafi nisan […]
Wata gyatuma mai shekara 91 ta kafa tarihi a wajen gasar tsere ta “Rock ‘n’ Roll” da aka gudanar a San Diego, inda cikin sa’o’i bakwai da mintuna bakwai da dakika 42 ta karade wuri mai nisan mil 26. Wannan tsdohuwa, mai suna Harriette Thompson da ta fito daga North Karolina, ta zama mafi nisan shekaru da ta taba yin irin wannan tseren cikin nasara. Wannan dai shi ne karo na 15 da take shiga gasar tsere.
Harriwette Thompson ta yi fama da cutar daji, don a cewarta an sha yi mata maganin rugugin sinadarai har sau tara a kafafuwanta.
Wannan tsohuwa, ta fara shiga gasar tsere, tun tana ’yar shekara 76, don tara kudi ga kawarta, wadda ta kamu da cutar daji.
Ta ce, mafi kyawon tsere, shi ne mutum ya kammala a kan lokaci.