Gyatuma ta kori barawo da sanda da ruwan zafi
Wata gyatuma ’yar shekara 83 da ke zaune a Houston ta kasar Amurka, ta fatattaki barawo da sanda da tafasasshen ruwa, bayan da ta yi masa kashedi ya ki ji, a ruwayar gidan talabijin na ABC, kmar yadda karamar tasharta ta KTRK-Tb ta ruwaito.“Sai n ace da shi, ‘wacce irin uwa gareka da ta raineka […]
Wata gyatuma ’yar shekara 83 da ke zaune a Houston ta kasar Amurka, ta fatattaki barawo da sanda da tafasasshen ruwa, bayan da ta yi masa kashedi ya ki ji, a ruwayar gidan talabijin na ABC, kmar yadda karamar tasharta ta KTRK-Tb ta ruwaito.
“Sai n ace da shi, ‘wacce irin uwa gareka da ta raineka har ka girma a irin wannan yanayi? Ya kamata a ce ka ji kunyar abin da ka aikata,” a cewar gyatuma Lillie McClendon, wadda ba da dadewa bat a kamala bikin cikar ranar haihuwar a karo na 83.
Wannan tsohuwa McClendon ta fito daga wanka, sai kawai taga tagarta a bude, kamar an shigo, a cewar KTRK. “Ban iya ganin fuskarsa ba, sai dai na ga idanunsa. Abin da kawai yake tambaya, ‘Ina kudi suke? Ina kudi suke?” inji McClendon.
Wannan mugun bako, nan dan ya shake gyatuma, a lokacin da yake tuhumarta ta bayyana masa inda ta boye kudinta. Ganin haka sai kawai ta fara kokarin kwatar ’yancinta. “to haka al’amarin yake. Ai ina da sanda, sai na dauko na fara caccakarsa,” injita. “Ina da tukunyar miya rowan zafi na tafarfasa a kan murhu,” a cewarta.
Nan da nan barawo ya yi ta kansa, ba tare da ya samu abin da yake nema ba.