Haƙƙoƙin ma’aikatan lafiya a wurin marasa lafiya
Akwai haƙƙoƙin kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar a zaman yarjejeniyar Geneva tun a shekarar 1949.
A yau kuma za mu duba irin hakkokin da suka rataya a kan marasa lafiya da ma danginsu ga mu ma’aikatan lafiya.
Mu ma ma’aikatan lafiya muna da hakkin daukar matakai na doka har ma da shigar da kara a daidaikunmu ko a kungiyance kan maras lafiya ko danginsa da suka bata mana.
- Yadda Dalar Amurka ke jefa ’yan Nijeriya cikin kunci
- Yadda noman kabewa ke azurta manoman Kano a lokacin karanci
Domin yanzu ana yawan samun labaran batanci da cin mutunci, a wasu lokuta ma har da dukan-kawo-wuka ga ma’aikatan lafiya.
Ga haƙƙoƙin namu kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar mana a zaman yarjejeniyar Geneva tun a shekarar 1949.
1. Duk ma’aikatan lafiya suna da haƙƙoƙin da doka ta ba wa kowane mutum kamar yadda yarjejeniyar Geneba ta tsara da kuma a cikin Kundin Tsarin Mulki na Amurka.
2. Ma’aikatan kiwon lafiya suna da ‘yancin samun halin mutuntawa daga marasa lafiyar da suke kulawa da su, kuma ya kasance suna da ‘yanci daga tsangwama, cin zarafi, kai musu hari, da maganganun batanci da zagi.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya suna da ‘yancin samun halin mutuntawa daga manyansu daga tsangwama da batanci ko zagi
4. Ma’aikatan kiwon lafiya suna da ‘yancin kare kansu daga hari.
5. Ma’aikatan kiwon lafiya suna da ‘yancin kai korafin majiyyaci ga hukumomin asibiti, idan ta kama kuma har ga hukumomi na gaba, kuma su bwannan korafi ta hanyar tsarin asibiti ko kuma a kotu ba tare da haɗari ga aikinsa ba.
6. Ba za a buƙaci ma’aikatan kiwon lafiya su sanya rayukansu ko lafiyar jikinsu, ko lafiyar iyalansu cikin haɗari ba.
7. Ma’aikatan kula da lafiya suna da haƙƙin samun isassun lokaci na sirri lokacin (break) wato lokacin cin abinci ko shan dan ruwa ko cin abinci ko Sallah kamar yadda suke buƙata.
Wadannan dokoki da ‘yanci kamar yadda aka gani, ‘yanci ne da dokokin duniya na Geneva wato Geneva Conbentions suka tsara mana.
A wannan kasa har yanzu babu wasu tsayayyun dokoki irin wadannan da aka tsara mana.
Wannan ce ma ta sa a bara Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa suka bukaci ‘yan majalisar tarayya na wannan jamhuriya da su taimaka su gabatar da dokoki irin wadannan na kare haƙƙoƙin ma’aikatan lafiya musamman ma ganin koke-koken ma’aikatan lafiya na hare-haren da aka kai musu a shekarar 2022 sun haura hare-hare 345.
An lura cewa kashi 65 cikin 100 na hare-haren sun faru ne sakamakon asarar marasa lafiya (mutuwa); 56 bisa dari saboda rashin halartar ma’aikatan lafiya da sauri (saboda yawan aiki); 41 cikin dari saboda rashin bayanai gamsassu; sai kuma kashi 28 cikin 100 saboda rashin isassun tsaro da sa ido daga hukumomin asibiti.