Haɗarin mota ya laƙume rayuka 6 da raunata wasu a Yobe
Haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 8 na dare a daidai lokacin da ‘yan kasuwar ke kan hanyarsu ta zuwa gida Jajere
An tabbatar da mutuwar mutane shida da wasu 15 sun samu raunuka daban-daban bayan da wata babbar motar ɗaukar kaya ta kufce wa direban ta yadda ta ƙauce hanya ta faɗi a Yobe.
Haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 8 na dare a daidai lokacin da ‘yan kasuwar ke kan hanyarsu ta zuwa gida Jajere a ƙaramar hukumar Fune bayan sun ci kasuwar shanu ta garin Potiskum da ake yi a ranar Laraba.
Wasu daga cikin fasinjojin da suka samu munanan raunuka an kai su asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu domin yi musu magani yayin da waɗanda ke da ƙananan raunuka ke samun kulawa a asibitin ƙwararru na Potiskum.
Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa na Jihar Yobe (YEMABUS) sun kasance a wurin don bayar da agajin gaggawa da kai waɗanda abin ya shafa asibiti da misalin ƙarfe 1 na dare zuwa Damaturu.