Haɗarin mota ya laƙume rayukan fasinjoji 15 a Kwara
Daya daga cikin motocin biyu da suka yi haɗarin na jigilar shanu da fasinjoji daga Ilorin babban birnin Jihar Kwara zuwa Ogbomoso Jihar Oyo,
Aƙalla mutum 15 ne rahotanni suka bayyana cewa sun rasa rayukansu a wani haɗarin mota da ya rutsa da wata tirela da wata mota a unguwar Oko Olowo da ke kan titin Ilorin zuwa Jebba a Jihar Kwara.
An samu rahoton cewa wasu da dama sun samu raunuka daban-daban a haɗarin motar da faru a ranar Laraba.
- Jeremiah Useni: Muhimman abubuwa kan ministan Abuja na zamanin Abacha
- Tinubu ya ba Ganduje da Gawuna shugabanci a Hukumar Filayen Jirage da Bankin gidaje
A cewar shaidun gani da ido, haɗarin ya rutsa da motoci biyu: wata tirela mai lamba AYE 218 XC wadda ta yi karo da wata motar fasinja mai lamba TTN 556 XA.
Motocin biyu, sun dai yi taho-mu-gama ne, yayin da suka yi karo da juna a yammacin ranar Laraba, kamar yadda aka bayyana.
An samu rahoton cewa, ɗaya daga cikin motoci biyu da suka yi haɗarin ya rutsa da su na jigilar shanu da fasinjoji daga Ilorin babban birnin Jihar Kwara zuwa Ogbomoso Jihar Oyo, yayin da tirelar ta taso daga Legas zuwa Kano.
An samu rahotan cewa jami’an bayar da agajin gaggawa da jami’an ‘yan sanda daga rundunar ‘yan sandan ‘G’ Division Oloje sun isa wurin a kan lokaci domin shawo kan lamarin, yayin da waɗanda suka jikkata aka garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
An yaɗa gawarwakin waɗanda abin ya shafa a cikin wani bidiyo da ke ta yawo a jihar da misalin ƙarfe 9 na daren ranar da lamarin ya faru tare da gawarwakin waɗanda abin ya rutsa da su a kan hanya.
Har yanzu dai Hukumar kiyaye haɗurra ta jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan hatsarin ba, tun bayan faruwar lamarin sai dai ta tabbatar da hakan ga majiyar jaridar Punch ta hanyar tattaunawa ta wayar tarho da wani babban jami’i a jihar.