Haɗarin mota ya yi ajalin mutum 6 a Ogun

An ga gawar wani mai sana’ar acaɓa da aka murƙushe kansa.

Haɗarin mota ya yi ajalin mutum 6 a Ogun

Mutum shida sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wasu haɗarurruka da suka auku a tsakanin daren Alhamis zuwa safiyar Juma’a a Jihar Ogun.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, haɗarin na farko wanda ya auku cikin dare a ranar Alhamis ya rutsa da wata mata mai juna biyu da wata dattijuwa da jikanta a unguwar Enugada da ke yankin Lafenwa a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Bayanai sun ce haɗarin dai ya rutsa da wata motar dakon kaya wadda ta sauka daga hanya ta kutsa kan wasu mutane da ke tafe a ƙasa a gefen hanya.

Wani faifan bidiyo da aka yaɗa ya nuna gawar wata mata mai juna biyu da aka murƙushe ƙafafunta a ƙasa.

Haka kuma, an ga wata gawar wani matuƙin babur mai sana’ar acaɓa da aka muƙushe kansa yayin da wata budurwa kuma aka mutsitsike ruwan cikinta.

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Nijeriya FRSC ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce mutane uku ne suka mutu.

Kakakin hukumar FRSC, Florence Okpe, a wata sanarwa da ta fitar, ta ce abin da ake zargin ya haddasa haɗarin birki ne ya tsinke wa babbar motar.

Kazalika, Okpe ta ce mutane uku sun jikkata a sanadiyyar haɗarin.

Ta ce an killace mamatan a ɗakin ajiye gawa, yayin da waɗanda suka samu raunuka ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.

Haka kuma haɗari na biyu wanda ya auku a washegari Juma’a, ya yi sandiyyar mutuwar mutane biyu har lahira a yankin Papalanto na jihar.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana