Haɗarin tirela ya kashe mutum 14 a Kano
Haɗarin ya afku ne a garin Imawa da ke Kura a kan hanyar Kano zuwa Kaduna jim kaɗan bayan idar da sallar Juma’a
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 14 a yayin da wata tirela ta afka masu bayan halartar sallar Juma’a a Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa haɗarin ya afku ne a garin Imawa da ke Ƙaramar Hukumar Kura ta jihar
Bayanai sun ce haɗarin wanda ya auku a kan hanyar Kano zuwa Kaduna ya faru ne jim kaɗan bayan idar da sallar Juma’a da misalin ƙarfe 13:50 na rana, inda tirelar wadda ta taho daga Kaduna ta ƙwace ta afka kan masallatan.
- Gini ya kashe mutum shida tare da jikkata wasu da dama
- Lakwaja: Birnin da manyan kogunan Nijeriya suka haɗu amma ba ruwan sha
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar FRSC reshen Kano, Abdullahi Labaran ya sanya wa hannu, ta ce an yi jana’izar tara daga cikin waɗanda suka mutu a yammacin Juma’a, yayin da waɗanda suka samu raunuka ke samun kulawa a yanzu haka a asibiti.
Sanarwar ta ce direban tirelar na nan a hannunsu.
Labaran ya ce, rundunar FRSC ta Jihar Kano ta aike da jami’anta zuwa wurin da lamarin ya faru ba tare da ɓata lokaci ba, tare da sauran jami’an tsaro, bayan samun wannan kiran na gaggawa, domin fara aikin ceto tare da bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.
Sanarwar ta ce, Kwamandan sashin Ibrahim Abdullahi, wanda ya jajanta wa iyalan mamatan, ya jaddada ƙudirin hukumar FRSC na tabbatar da tsaro a kan titi.
Ya kuma buƙaci duk masu amfani da hanyoyin da su bi ƙa’idojin zirga-zirga domin gujewa afkuwar irin wannan iftila’in.